Jama'a daga Kasashen Duniya 90 Sun Saye Hannun Jari a Matatar Dangote

Jama'a daga Kasashen Duniya 90 Sun Saye Hannun Jari a Matatar Dangote

  • Matatar Aliko Dangote ta jawo hankalin masu zuba jari daga kasashe 90, ciki har da kasashen Afirka 51
  • Kamfanin ya samu kudin shiga na dala biliyan 22.5 da ribar dala biliyan 4.7 cikin watanni tara na shekarar bana
  • Ana sa ran kammala sayar da hannun jarin a ranar 27 ga Oktoba, 2026, kamfanin bai shirin kara wa'adin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Matatar man fetur ta Dangote ta jawo jama’a daga duniya bayan sanar da shirin sayar da hannun jarin ta ga jama'a.

Wannan tsarin kasuwanci ya jawo hankalin masu zuba jari daga kasashe sama da 90 a fadin duniya da suke so su ma a dama da su.

Dangote IPO
Aliko Dangote da manyan kamfaninsa lokacin da aka bude IPO Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hannun jari: An jawo mutane daga kasashe 90

Kamfanin ya bayyana cewa masu zuba jarin sun fito daga kasashen Afrika 51 cikin 54 kamar yadda muka karanta a Business Day.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ziyarci Yari da labaran karya da suka yi ta yawo a makon da ya wuce

Dangote ya ce wannan ya nuna yadda 'yan Afrika ke kara sha'awar mallakar manyan masana'antun da ake ginawa a nahiyar.

Kusan a kasashe uku ne kawai na Afrika ba a samu wadanda suka sa kudinsu a juya a matatar man da babu kamar ta nahiyar ba.

Dangote ya kafa tarihi a harkar hannun jari

A cewar kamfanin, shirin sayar da hannun jarin ya kafa sabon tarihi a kasuwar hannayen jari tun ranar da aka bude shi.

A kwanaki 10 na farko, matatar ta kafa tarihin da ba a taba ganin irin shi a kasashen ba.

Masu sha'awar sayen hannun jarin sun hada da daidaikun mutane, asusun fansho da kuma manyan hukumomin zuba jari.

Sauran wadanda suka kawo kudinsu su ne masu kula da kadarori, gwamnatoci a madadin jama’a da sauran masu zuba jari.

Mene ne dalilin saida hannun jarin matatar Dangote?

Babban jami'in kula da harkokin kudi na rukunin kamfanonin Dangote, Murat Erden, ya ce ba kudin mutane kawai ake nema ba.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun shari'ar Musulunci ta tilasta matashi share babban masallacin Juma'a

Punch ta rahoto shi yace shirin ya ba 'yan mahiyar da masu zuba jari daga sauran sassan duniya damar mallakar kaso a Dangote.

Rahoton ya ce matatar ta samu kudin shiga na dala biliyan 22.5, tare da ribar dala biliyan 4.7, a watanni tara na shekarar bana.

Kudin da ake samu a matatar Dangote a yau

Wannan ya nuna sauyi mai girma idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2025 da ya yi asarar dala miliyan 117.2.

Kudin shigar kamfanin sun karu da kashi 144 cikin 100, daga dala biliyan 9.2 zuwa dala biliyan 22.5 a shekarar da ake ciki.

Haka kuma, kudin da yake samu daga ayyukansa kafin cire wasu haraji da sauransu sun karu kusan ninki tara, zuwa dala biliyan 5.5.

Bayan kara wa’adi, ana sa ran kammala sayar da hannun jarin a ranar 27 ga Oktoba, 2026.

Matatar ta nanata cewa a halin yanzu ba ta shirya kara wa'adin sayar da hannun jarin ba, za a rufe kofa a Oktoban nan.

Dangote
Wani bangare na matatar Dangote a Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matatar Dangote ta soma saida hannun jari

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama wasu matasa 2 da ba a yi tsammani ba ɗauke da bindiga a Kano

A tsakiyar Satumba aka ji labari matatar Dangote ta fara sayar da sababbin hannun jari guda biliyan 4.1 a kan farashin N525.

Ana sa ran tara kusan Naira tiriliyan 2.15 domin fadada ayyukan matatar da aka bude a 2023 da kuma bunkasa tattalin arziki.

An tsara ci gaba da sayar da hannun jarin har zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2026, kuma mafi ƙarancin adadin siye shi ne 10 kan N5,250.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng