Ana Shirin Fito da Makudan Kudi da Suka Wuce Tunani don Raba Wa Yan Arewa a Zaben 2027
- Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da wulaƙanta ’yan Arewa da kuma yin watsi da su
- Ya yi zargin cewa magoya bayan Tinubu da APC na shirin raba kuɗi masu yawa domin samun goyon bayan ’yan Arewa
- Baba-Ahmed ya buƙaci ’yan Arewa su kare mutuncinsu, su ƙi karɓar kuɗin da za a yi amfani da su wajen rinjayar zaɓinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hakeem Baba-Ahmed, shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da wulaƙanta ’yan Arewa da yin watsi da su.
Hakeem Baba Ahmed ya gargaɗi magoya bayan shugaban ƙasar kan yunƙurin neman ƙuri’u ta hanyar raba kuɗi a babban zaben 2027.

Source: Twitter
Baba-Ahmed ya yi wannan zargi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi iƙirarin cewa magoya bayan Tinubu da APC na shirin raba kuɗi fiye da yadda aka taɓa gani a baya domin samun goyon baya a Arewa.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An ji yadda Buhari ya nuna akwai matsala idan Tinubu ya karbi mulki a 2023
Yadda ake shirin sayen kuri'un Arewa
Ya ƙalubalanci shugabannin siyasa daga jihohin Arewa da ke goyon bayan Shugaba Tinubu da su bayyana wa masu zaɓe dalilin matsayinsu.
“Me yan kamfen ɗin dawo da Tinubu da APC za su gaya wa jama’a, musamman waɗanda suka fito daga jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto, Katsina, Borno, Yobe, Kwara, Kaduna, Plateau, Kogi da Nasarawa?
“Mun san za su raba kuɗi fiye da yadda aka taɓa gani a siyasar Najeriya. Matsalarsu ita ce suna raina ’yan Arewa. Suna ganin za su iya sayen mu da kuɗi, su sa mu manta da wulaƙanci da rashin kulawar da muka fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.”
Baba-Ahmed ya gargadi yan Arewa
Shugaban PRP na ƙasa ya buƙaci ’yan Arewa su kare mutuncinsu, su kuma ƙi duk wani yunƙuri na amfani da kuɗi wajen sayen kuri'unsu.
“Za mu nuna musu cewa mu ma ’yan Adam ne masu mutunci. Idan muka ƙi APC da Tinubu, kada wani ya kuskura ya yi maguɗi wajen sauya sakamakon zaɓe,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Shin Tinubu ya karya doka da ya ce ba zai je kamfe wasu jihohin Najeriya ba? An samu bayani
Baba-Ahmed ya kuma ƙalubalanci magoya bayan shugaban ƙasar da su kare matsayinsu na siyasa, inda ya bayyana cewa ya kamata a bai wa kowane ɓangare damar fafatawa gabanin zaɓe.

Source: Twitter
Ya kammala saƙonsa da addu’ar Allah Ya kuɓutar da ’yan Najeriya daga shugabannin da ke zaluntar jama’a.
Yadda Buhari ya fahimci illar Tinubu
Kun ji cewa ana ganin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fahimci illar da Bola Ahmed Tinubu zai iya yi wa Najeriya shi yasa ya kokarin hana shi zama magajinsa a zaben 2023.
Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa Buhari ya yi kokarin dakile duk wata matsin lamba kan Tinubu ya gaje shi saboda ya san zai cutar da Najeriya.
Asali: Legit.ng