Magana Ta Fito: An Ji Yadda Buhari Ya Nuna Akwai Matsala idan Tinubu Ya Karbi Mulki a 2023

Magana Ta Fito: An Ji Yadda Buhari Ya Nuna Akwai Matsala idan Tinubu Ya Karbi Mulki a 2023

  • Hakeem Baba-Ahmed ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kokrin shanye matsin lambar masu son Bola Tinubu ya gaje shi
  • Shugaban PRP ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa Najeriya cikin mawuyacin hali, hana mai kira ga ’yan Najeriya su canza shi
  • Ya kuma soki gwamnonin Arewa bisa gazawarsu wajen jawo hankalin Tinubu kan matsalolin tattalin arziki da rashin gamsuwar jama’a a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fahimci illar da Bola Ahmed Tinubu zai iya yi wa Najeriya shi yasa ya kokarin hana shi zama magajinsa.

Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa Buhari ya yi kokarin dakile duk wata matsin lamba kan Tinubu ya gaje shi saboda ya san zai cutar da Najeriya.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya zube kasa warwas a Najeriya saboda tsare tsaren Tinubu'

Hakeem Baba Ahmed.
Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed Hoto: Hakeem Baba Ahmed
Source: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa Hakeem Baba-Ahmed ya yi wannan ikirari ne a wani taron koli da Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta shirya.

Baba Ahmed ya caccaki Tinubu

Ya kuma zargi Tinubu da kai Najeriya matakin da ba ta taɓa kai wa ba na tabarbarewa a ƙarƙashin gwamnatinsa.

Ya dage cewa dole ne ’yan Najeriya su hana burin shugaban ƙasa na sake yin wa’adi ya rinjayi muradun ƙasa.

A cikin wani bidiyo na taron da aka wallafa a tashar YouTube ta Symfoni, shugaban PRP ya ce ya kamata ’yan Najeriya su tambayi kansu irin illar da burin Tinubu na zama shugaban ƙasa zai iya haifarwa tun lokacin da ya bayyana kalmar “Emilokan”.

Kalmar Yarbanci ce da ke nufin “lokacina ne”, wadda ta shahara a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023.

Baba-Ahmed ya ce:

“Ko Buhari ma yana ganin Tinubu ba alheri ba ne ga wannan ƙasa. A gaskiya, Buhari ba ya tare da shi. Buhari ya yi tsaye wa wasu mutane da suka dage cewa lallai Tinubu ne ya kamata ya zama shugaban ƙasa.”

Kara karanta wannan

Gwamna ya shirya kayar da Tinubu a jihohi 12 a zaben shugaban ƙasa na 2027

Tambayoyi kan taken Emilokan

Baba-Ahmed ya yi tambaya kan dalilin amfani da wannan taken, yana mai cewa bai kamata a ɗauki shugabancin ƙasa mai kusan mutane miliyan 250 a matsayin wani haƙƙin da mutum zai ce dole sai ya samu ba.

Ya kara da cewa:

"Ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa akwai matsala tun ranar da Tinubu ya ce ‘lokacina ne’. Wataƙila mun yi kuskure da ba mu lura ba.
“Muna da shugabancin ƙasa mai mutane miliyan 250. Lokacina ne? Don yin me? Don zama shugaban ƙasa?”
Tinubu da Buhari.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da marigayi Muhammadu Buhari Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Ya ce Najeriya ta shafe tsawon lokaci tana fuskantar wahalhalu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Ya zargi gwamnatin da gaza cimma nasara a muhimman fannoni da ake amfani da su wajen auna ci gaban ƙasa.

Yan adawa za su hada kai kafin 2027

Kun ji cewa Salihu Lukman ya ce jam’iyyun adawa za su fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya kafin ranar babban zaɓen 2027.

A cewarsa, ƙoƙarin haɗin kan ya wuce jam’iyyu shida da ke cikin shirin a halin yanzu, ya ce suna ƙoƙarin faɗaɗa haɗin gwiwar ta hanyar tuntuɓar sauran jam’iyyun siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262