Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

  • Wani bidiyo da cikin kwanakin nan yake ta yawo a soshiyal midiya ya bayyana wani irin kitson budurwa mai bada mamaki
  • A bidiyon da yanzu ya yadu, an ga budurwar da kitson rabin kanta yayin da ta gaba aka yi mishi kwal babu ko gashi daya a kai
  • Mutane da yawa dake amfani da kafar sada zumuntar zamani sun dinga tsokacin zolaya inda wasu ke cewa Mortal Kombat ya dawo

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gayu ya banbanta a wurin jama'a da dama kuma ma'anarsa daban ce ga kowanne mutum. Hakan yasa gayun mutane da yawa ya banbanta, ya zama ba irin na kowa da kowa ba.

Wata budurwa cikin kwanakin nan ta zama abun magana bayan bidiyonta ya karade kafafen sada zumuntar zamani inda ta bayyana a wani wuri mai kama da kasuwa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

Hairstyle
Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce. Hoto daga @gossipmilltv
Asali: Instagram

A bidiyon da @gossipmilltv suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga budurwar sanye da dogon wando tare da riga mai kananan layika.

Yayin da shigarta bata wani ja hankali ba, tsari da zabin kitsonta shi ne ya janyo maganganu daga jama'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yawan kanta ya tabbata a saiko, amma daga tsakiya kawai sai ga wani irin karin gashi da ta saka mai launin fari.

Kalla bidiyon a kasa:

Jama'a tuni suka dinga bayyana ra'ayoyinsu tare da martani kala-kala a kan wannan zabin kitson.

Mimiokeren1:

"A gaskiya tayi kyau, wannan salon Afrika ne. Ina kaunarsa."

Hellenbaylon:

"Ina kaunar irin kitsonta."

Iamkingdinero2:

"Ce min mortal Kombat, kada ki wuce hakan."

Ronaldcreative:

"Gashin karawa yanzu tsada gare shi."

Official_no_worries_yrn:

"Ta sa na tuna wannan mutumin na mortal Kombat."

riamz:

"Ku tsaya, ta kuwa san abinda ke tsakar kanta?"

Kara karanta wannan

Bidiyo: Hazikin Yaro Mai Shekaru 3 Yana Kacaccala Lissafi Ya Birge Jama'a

Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa kyakyawa a TikTok wacce ke aiki matsayin 'yar aiki a Dubai tayi bidiyo inda take yi wa masu mata dariya martani.

Tace mutane suna mamakin dalilin da yasa take 'yar aikin gida a Dubai duk da zata iya samun kudi da irin diri da surar da take da shi.

A martanin jama'a kan ra'ayinta akan aikin da take yi, budurwar ta bayyana cewa bata damu ba kuma ta mayar da hankali kan abinda ya kai ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel