Abun Al Ajabi
Wani bidiyo da ya yadu ya nuno yadda mazauna wata unguwa a Najeriya suka haddasa dirama bayan ganin wani mutumi mai kama da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wata matashiyar budurwa wacce ke biyan N800k na hayar gidanta duk shekara a Legas ta ce bata da matsalar wutan lantarki a unguwarta. Mutane sun sha mamaki.
Wasu matasa sun yi aikin dana-sani yayin da suka sace wata yarinya a jihar Kano tare da tafiya da ita jihar Katsina, Sun nemi a basu kudin fansa miliyan 2.
Wata mata mai aiki a jami'a ta bayyana shiga tashin hankali yayin da take murnar samun karuwa, ta haifi jarirai biyar a nan take, ta bayyana bashin da ke kanta.
Wani matashi ya nuna fikirar da Allah ya yi masa ta hanyar kera wata kalar motar da ba a taba ganin irinta ba. Ya tuka ta aikin unguwarus, mutane sun yi mamaki.
Wani dan arewa ya bayyana bukatar aure, zai ba da sadakin Naira miliyan daya da kuma karin N200,000 don rage mata radadin hana ta yin wasu bukukuwan bidi'a.
Wani likitan Najeriya ya baiwa wata mata da ta nuna sha’awarta na son haihuwar tagwaye shawarar abun yi. Ya bukaci da ya je jihar Oyo sannan ta ci doyarsu.
Wani dan gajeren bidiyo ya nuno wani matashi da abokansa suna taya shi murnar siyan sabuwar mota. Mai motar ya dinka riga dauke da katon logon Benz a gabansa.
Wata hazikar budurwa yar Najeriya ta je soshiyal midiya don nuna wa mutane yadda ta yi fentin gidanta da kanta bayan ta yi hade-haden da ya dace da dakinta.
Abun Al Ajabi
Samu kari