Labarin Tagwayen da Suka Zo Duniya tare Suka Rasu kusan Lokaci Duda daga Ciwo tare

Labarin Tagwayen da Suka Zo Duniya tare Suka Rasu kusan Lokaci Duda daga Ciwo tare

  • Dr. Hadiyah Usman da Dr. Aidah Usman tagwaye ne da aka haifa shekaru kusan 30 da suka gabata
  • Wadannan yara sun zo duniya da cutar sikila, amma a haka suka yi karatu har suka fara aikin asibiti
  • Ciwon su ya tashi lokaci guda har ya zama ajalin Aidah, a sanadiyyar haka ita ma Hadiyah ta rasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Yobe - Wasu tagwaye da suka shekar 28 a duniya sun ce ga garinku nan a cikin kasa da mako daya duk da ba a wuri guda suke ba.

Dr. Hadiyah Usman da Dr. Aidah Usman tagwaye ne ‘ya ‘yan Farfesa Hadiza Abdullahi Usman da kuma Farfesa Usman Abdullahi.

Dr Hadiyah da Dr Aidah Usman
Marigayiya Dr Hadiyah da Marigayiya Dr Aidah Usman da hoton tagwayen suna yara Hoto: Adamu Abdulrahman Iguda (Facebook)
Source: Facebook

Rasuwar 'yan biyun Farfesa Usman Abdullahi a Nguru

A shafin Facebook Adamu Abdulrahman Iguda ya bada labarin yadda wadannan ‘yan biyu suka rasu, kwanaki biyu ne a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu da abokinsa suka kusa fada wa gadar Legas a hadarin mota

Mutane da-dama sun tausaya iyalin farfesan da ‘yanuwan tagwayen. Tuni dai an birne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Daily Trust ta rahoto cewa Hadiyah Usman wanda likita ce ta fara kwantawa rashin lafiyarta ta amosarin jini wanda suke fama da shi.

An yi jinyar ta a asibitin tarayya na Nguru, inda mahaifinsu Farfesa Usman Abdullahi yake aiki a matsayin babban kwararren likita.

Ita kan ta mahaifiyarsu ita ce tsohuwar shugabar wannan babban asibiti da yake jihar Yobe.

Majiya ta ce bayan dan lokaci Hidayah ta cika a ranar Juma’a, kuma aka birne ta bayan yi mata sallah a fadar Sarkin Nguru kashegari.

'Yan biyun sun saba yin rashin lafiya tare

Ita ma ‘yar uwarta Aidah ciwon nata wanda aka fi sani da sikilar ya tashi a lokacin, ita tana kwance a asibitin koyarwa a Maiduguri.

‘Yanuwan mamatan sun ce wannan ba abin mamaki ba ne, domin an saba jin sun yi ciwo a lokaci daya ko da ba su tare da juna.

Kara karanta wannan

Iyaye sun shiga ha’ula’i, ‘yan bindiga sun bukaci N950m kafin sakin masu NYSC

"Kai har gidan sun saba da hakan. Duk lokacin da daya yake ciwo, iyayen sun san shi ma ‘yan biyun zai kwanta rashin lafiya."

- in ji 'yanuwansu

Aidah ta warke bayan Hadiya ta rasu a Nguru

Da Dr. Aidah ta warke aka sallame ta daga asibitin da ke jami’ar Maiduguri, sai ta wuce garin Nguru domin yin makokin ‘yaruwarta.

Tana isa gidan, sai ta matsa cewa za ta ziyarci kabarin ‘yaruwarta domin yi mata addu’a. Ashe ajali ne yake kiranta bayan 'yan sa'o'i.

Da farko mahaifiyarta wanda likita ce ta nuna adawarta, amma a karshe ta hakura ganin yadda Dr. Aidah ta dage sai ta je makabartar.

Yadda Aidah ta ki barin kabarin marigayiya Hidayah

Kawun yaran, Ibrahim Hasbunallah ya ce sun ziyarci kabarin tare da mijin mai rasuwa da kanwarsu amma sai Aidah ta ki barin kabarin.

Da aka gama addu’a sai ta ce sai ta bi ‘yaruwarta, ana haka sai ta fara jijjiga a karshe aka ruga da ita zuwa asibiti wurin karfe 3:30 na maraice.

Zuwa karfe 4:10 na yamma, an gama sallar la’sar kenan ita ma sai ta cika a sashen ICU a asibitin. Mutuwar tagwayen ta girgiza jama'a.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Hasbunallah ya bada labarin yadda tagwayen suka karanci ilmin likitanci da na harkar magunguna a jami'ar Maiduguri duk da ciwonsu.

An yi garkuwa da 'yan NYSC 19

Ana da rahoto cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan bautar kasa (NYSC) a hanyarsu ta zuwa sansanin horaswa a jihohin Akwa Ibom da Abia.

Miyagun sun soma kiran iyayen matasan, sun bukaci kudin fansa har Naira miliyan 950 domin sako su, daga baya an ce an rage abin da ake nema.

A dandalin X, abokai sun baza kokon bara domin mutane su tara N50m da za a biya a matsayin kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng