Matashin Miloniya Ya Baro Motar Marsandi Sabuwa Dal, Ya Dinka Kaya Da Logon Benz a Bidiyo

Matashin Miloniya Ya Baro Motar Marsandi Sabuwa Dal, Ya Dinka Kaya Da Logon Benz a Bidiyo

  • Wani matashi ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a TikTok bayan ya baje kolin sabuwar motarsa kirar Marsandi
  • Mutane da dama sun cika da mamakin ganin yadda ya wakilci kamfanin motar da ya siya inda ya dinka kaya dauke da logon Benz a jiki
  • Daga cikin wadanda suka kalli bidiyonsa tare da abokansa a gaban motan sun nemi sanin tushen arzikinsa

Wani matashin miloniya mai suna @sanousasawadogo, wanda ya siya mota kirar Marsandi Benz ya baje ta a wani bidiyo yayin da abokansa ke taya shi murna.

A farkon bidiyon na TikTok, an gano shi tsaye ya kame a gaban motar sanye da riga mai dauke da logon Benz don nuna cewa shi ne mamallakin motar.

Matashi da abokansa a jikin mota
Matashin Miloniya Ya Baro Motar Marsandi Sabuwa Dal, Ya Dinka Kaya Da Logon Benz a Bidiyo Hoto: TikTok/@sanousasawadogo
Asali: UGC

A shafi na biyu na bidiyon mai ban dariya, masu masa fatan alkhairi sun kame jikin motar yayin da an saka motar Benz din tana tafiya a hankali.

Kara karanta wannan

Dan Mai Karfi: Bakanike Mai Daukar Injin Mota Shi Kadai Ya Bayyana a Bidiyo

Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa wannan shi ake kira da "kudi ya yi batan hanya" yayin da suke mamakin wani irin aiki yake yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Omos ya ce:

"Mutumina ya sanya logon Benz a jikin kayansa."

Nasa Austin ya ce:

"Wata motar a mugun hannu."

Face ta ce:

"Ainahin bayanin kana iya kasance da kudi amma baka da aji."

Victory ya ce:

"Ya kai kanka ka yi amfani da logon Benz wajen dinka riga da wando."

Matashi ya kera motar wasan tsere da hannunsa, ya tuka a bidiyo

A wani labari na daban, wani matashin saurayi ya sha jinjina a shafukan soshiyal midiya bayan mutane sun ci karo da bidiyonsa yana tuka wata motar wasan tsere wanda ya kera da hannunsa a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

Mutane da dama sun nuna takacicinsu cewa lallai Allah ya albarkaci Najeriya da tarin hazikai amma babu shugabanni nagari da za su tallafa masu don ganin sun zama wasu a rayuwa ta hanyar zuba jari a kansu.

An gano taron mutane da suka yayyame matashin yayin da suke nuna mamaki da sha'awarsu a kan wannan namijin kokari da ya yi. Wasu sun tattaba motar don jin yadda abun yake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel