Ki Siya Doyansu Ki Ci: Likita Ya Fada ma Mata Masu Son Haihuwar Tagwaye Hanyar Da Za Su Bi

Ki Siya Doyansu Ki Ci: Likita Ya Fada ma Mata Masu Son Haihuwar Tagwaye Hanyar Da Za Su Bi

  • Wani likitan Najeriya ya yi martani ga wata mata a Twitter wacce ta nuna burinta na son haihuwar tagwaye
  • A wallafarsa, ya bukaceta da ya je Igboora a jihar Oyo wanda ya yi ikirarin cewa nan ne cibiyar tagwaye na duniya
  • Likitan ya bayar da shawarar cewa cin doyarsu da miyar Ilasa zai sa mutum ya haifi tagwaye

Wani likitan Najeriya mai suna @thebeardedDrSina a Twitter ya yadu bayan ya bayar da shawara kan hanyar da za a bi don samun haihuwar tagwaye.

Ya yi ikirarin cewa kowa zai iya haihuwar tagwaye ta hanyar cin doya da miyan Ilasa akai akai a garin Igboora a jihar Oyo.

Likita da mace dauke da tagwaye
Ki Siya Doyansu Ki Ci: Likita Ya Fada ma Mata Masu Son Haihuwar Tagwaye Hanyar Da Za Su Bi Hoto: Tim Hall, FS Productions/Getty Images
Asali: UGC

Ya bayyana Igboora ta jihar Oyo a matsayin cibiyar tagwaye na duniya, yana mai cewa kowa na iya mallakar tagwaye a wannan yankin, domin hatta dabbobi haihuwar tagwaye suke yi.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

Domin karfafa ikirarinsa, ya ce zai daina aikin likitanci idan shawarar da ya bayar bai yi aiki ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ki je Igboora a jihar Oyo, cibiyar tagwaye na duniya. Ki siya doyansu, ki ci da kyau sannan ki ci miyarsu ta Ilasa akai-akai. Idan baki haifi tagwaye a shekara daya ba, zan daina aikin likita ci.”

Dr Sina ya yi karin haske game da Igboora

A wata wallafa da ya yi a baya, Dr. Sina ya yi ikirarin cewa doya na dauke da ‘clomiphene’ wanda ke sa mata samar da kwan haihuwa, don haka yana kara damar da mace ke da shi na haihuwar tagwaye.

Likitan ya ce Igboora na da tagwaye da dama cewa hatta dabbobi irin su akuyoyi, tunani, da sauransu suna haihuwar tagwaye.

Jama’a sun yi martani

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

@Yinkzworld2 ya yi martani:

“Igboora kasa ce ta tagwaye, wanda Allah kadai ne ya san abun al’ajabin da ke tattare da wannan. Babu wani iyali da baida tagwaye kuma ina shakku idan akwai juya a wannan kasa. Yana daya daga cikin abun al’ajabin da kimiyya ma ba za ta iya bayar da cikakken amsa ba a kai.”

@alexlobaloba ya ce:

“Likita ya yi gaskiya, Igbo-Ora kasa ce ta haihuwa kuma cibiyar tagwaye ta duniya.”

@fovrfay ta yi martani:

“Ya batun yan uku, tambaya nake yi har zuciyata.”

@Wole_xy ya rubuta:

“Na gwada kuma na tabbatar. Tagwayena na nan lafiya.”

Legit.ng ta tuntubi wata yar yankin don jin ta bakinta inda ta tabbatar da cewar haka abun yake domin dai a cewarta kowani gida ka je akwai tagwaye.

Misis Funmi Okutade ta ce:

“Ni yar asalin Igbo-ora ce amma ina zama ne a nan Legas. Da gaske ne koina ka shiga a garinmu sai ka samu yan biyu shiyasa ake mana lakabi da gidan tagwaye, wannan wata baiwa ce da Allah ya yi mana. Kuma da gaske ne idan dai ka ci miyan kauyenmu mai suna ‘Ilasa’ zai taimaka maka wajen haihuwar yan biyu.”

A wani labari na daban, wani uba ya kulla yarjejeniya da karamar diyarsa a kokarinsa na hana ta kula saurayi har sai nan da shekarar 2041.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng