Bayan Shekaru 6 Yana Ɓuya, Dubun Ɗan Tsohon Shugaban PRTT, Maina Ta Cika a Abuja

Bayan Shekaru 6 Yana Ɓuya, Dubun Ɗan Tsohon Shugaban PRTT, Maina Ta Cika a Abuja

  • Hukumar DSS ta kama Faisal, ɗan tsohon shugaban kwamitin sake fasalin fansho na Najeriya (PRTT), Abdulrasheed Maina a Abuja
  • Majiyoyi sun ce an miƙa wanda aka kama ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'adi (EFCC) domin ci gaba da bincike
  • Faisal ya tsere tun shekarar 2020 bayan fuskantar tuhuma kan halasta kuɗaɗen haram amma yanzu ann kama shi ne a yankin Karsana da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta kama Faisal, ɗan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin da aka kafa domin sake fasalin tsarin fansho (PRTT).

Jami'an DSS sun kama Faisal ne bayan tsawon shekaru ana nemansa, sakamakon tsallake sharuddan belin fa ya yi, ya tsere daga Najeriya.

Faisal Maina.
Bayan Shekaru 6 Yana Ɓuya, Dubun Ɗan Tsohon Shugaban PRTT, Maina Ta Cika a Abuja
Source: Twitter

Majiyoyi sun shaida wa jaridar The Cable cewa hukumar DSS ta miƙa Faisal ga Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC).

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro kan 2027, ya aika sako ga Atiku da sauransu

Wata majiya ta bayyana cewa:

“An kama shi ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa Faisal ya dawo ƙasar a ɓoye.”

Faisal, wanda ya kasance a ɓoye tun shekarar 2020, ya taɓa gurfana a gaban kotu bayan EFCC ta shigar da shi ƙara bisa tuhume-tuhume uku da suka shafi halasta kuɗaɗen haram.

Bayanan da The Cable ta samu sun nuna cewa jami’an DSS sun bi diddigin Faisal tare da kama shi a yankin Karsana da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262