Yan Najeriya Sun Gano Mai Kama Da Shugaba Buhari Yana Tafiya a Titi, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Yan Najeriya Sun Gano Mai Kama Da Shugaba Buhari Yana Tafiya a Titi, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Wani bidiyo da ya yadu a manhajar TikTok ya nuno lokacin da wani mutum cikin shiga irin ta Shugaba Buhari ya fito titin unguwa
  • A cikin bidiyon, an gano mutumin yana tafiya a titin unguwar yayin da wasu mutane suka taru don kada ayi babu su
  • Dan gajeren bidiyon ya kuma nuno shi yana dagawa mutane da ke tsaye a gaban shagunansu wadanda suka zata shi din shugaban kasa ne hannu

Wani mutumi da ya badda kamanninsa ya koma sak kamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yadu a soshiyal midiya.

A bidiyon da yadu, an gano mai kama da Buharin yana karfafawa matasan Najeriya gwiwa yayin da wasu ke kallonsa dauke da murmushi a fuskokinsu.

Mai kama da Buhari kewaye da mutane
Yan Najeriya Sun Gano Mai Kama Da Shugaba Buhari Yana Tafiya a Titi, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce Hoto: @buhariangus/TikTok
Asali: UGC

Wasu ganau sun zata shi din shugaban kasa ne sannan sun ta daga masa hannu a bidiyon, suna jinjina masa yayin da saura ke kallo cike da rudu.

Kara karanta wannan

Tsantsar fikira: Bidiyon yadda matashi ya kera motar da ba a taba ganin irinta ba, ya tuka ta

Yayin da mutane ke kallon shi, ya tsayar da wata matashiyar yarinya wacce ke tafiya cikin sauri don tattaunawa da ita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yana ta jaddada cewar matasa sune manyan gobe. Ya kuma jinjinawa matasa a unguwar yayin da yake wucewa sannan mutane suka yi masa zuruu da ido.

Jama’a sun yi martani

@She’dsurvived ta ce:

“Ni dan Liberiya ne kuma na ji maganganu sosai a kan Buhari amma damuwata shine wakar mai ban dariya.

@Catherine.Engineer ta rubuta:

“Ya kamata Baba ya aikawa gayen nan 10m don ya gyara kansa.”

@user Brazzaville ya yi martani:

“Har yanzu ina cikin rudani faaa. Kwafin Buhari na da yawa a duniya faaa. Me yasa basu dauki wannan ba, suka je suka dauko daga Sudan.”

@Shakira ta yi martani:

“Kada su je su kashe ka su yi tunanin Buhari ne.”

Kara karanta wannan

Yaro Da Kudi: Matashin Miloniya Ya Siya Motar Marsandi Sabuwa, Ya Dinka Kaya Dauke Da Logon Benz a Bidiyo

@rejoice Ifechukwu ta yi martani:

“Na zata yan Indiya me kawai ke da masu kama da su.”

Kalli bidiyon a kasa:

Yaro ya yi wa likita kallon uku saura kwata bayan ya masa allura

A wani labari na daban, jama'a su tofa albarkacin bakunansu bayan sun ci karo da bidiyon wani karamin yaro da aka tsirawa allura.

Maimakon ya bare baki yana kuka yadda yara ke yi, sai aka gano shi ya dake yayin da ya yi wa likitan kallon uku saura kwata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel