Hazikin Dan Najeriya Ya Tattara Karkacen Karafa, Ya Kera Wata Kalar Mota Mai Daukar Hankali

Hazikin Dan Najeriya Ya Tattara Karkacen Karafa, Ya Kera Wata Kalar Mota Mai Daukar Hankali

  • Wani matashi dan Najeriya ya nuna hazakar da Allah ya yi masa ta hanyar kera mota da tarkacen karafa guntaye kusan marasa amfani
  • An ga bidiyon lokacin da matashin ke gwada motar a unguwarsu a shafin Instagram kuma 'yan Najeriya da yawa sun shiga mamaki, sun yaba masa
  • Ana yawan samun lokuta irin wannan da matasan Najeriya ke amfani da hazakarsu wajen kirkirar abubuwan ban mamaki

Wani dan Najeriya ya bar jama'ar baki bude a shafukan sada zumunta lokacin da aka ga kalar motar da ya kera wata da tarkacen karfe mara amfani.

A cikin wani faifan bidiyo da aka yada a Instagram ranar 15 ga Disamba, @onlynuelpls, ya nuna lokacin da matashin ke tuka motar akan titin garinsu.

Hazikin matashi ya kirkiri mota
Hazikin Dan Najeriya Ya Tattara Karkacen Karafa, Ya Kera Wata Kalar Mota Mai Daukar Hankali | Hoto: @onlynuelpls
Asali: Instagram

Motar da aka kera da karfe

A faifan bidiyon, an ga motar da matashin ya kera a tsaye babu kofa balle wani rufi, kawai a bude take kowa ya sha iska.

Kara karanta wannan

Yaro Da Kudi: Matashin Miloniya Ya Siya Motar Marsandi Sabuwa, Ya Dinka Kaya Dauke Da Logon Benz a Bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan Najeriya da dama sun ce ya burge su kuma sun yaba masa bisa irin fikira da yake da iya, sun yi martani da yawa mai daukar hankali.

Kalli bidiyon:

Jama'ar Instagram sun yi martani

@clearcut_lawncare ya ce:

"Dan uwa ya sanya jirgin ruwan da ba a iya gani yana motsi."

@onosedvgbd ya ce:

"Idan da ace manyan mutanenmu za su saka hannun jari a irin wannan tsagwaran basira."

@tylereick 97 ya ce:

"Dan uwa kana tuka kwarangwal kawai."

@logan_olm ya ce:

"Mutumin ya sami sabuwa Lamborghini, Allah ida nufi."

@jasonsntony13 ya ce:

"Wannan abin ban mamaki ne, babu tsaro amma abin ban mamaki ne. Kasancewar yana da wannan fikiri, ya kenan idan yana da wadata. ”

@i_love_my_ninja ya ce:

“Ku sama wa wannan mutumin aiki! Idan ya kera wannan to ya cancanci aiki inda zai yi amfani da wannan ilimin!!"

Kara karanta wannan

Dan Mai Karfi: Bakanike Mai Daukar Injin Mota Shi Kadai Ya Bayyana a Bidiyo

@steelcity33ce4life ya ce:

"Wasu mutane suna ta dariya game wannan amma hanyar kera wannan abin ban mamaki ne."

@xdjohn738 ya ce:

"Abu mai kyau ba ya sauka a Afirka."

@yoshikage said:

"Babu nauyi, ingantacciyar hanyar amfani da mai."

A Najeriya kuwa, gwamnati za ta kaddamar da jirgi mai saukar ungulu na farko da aka kera kuma aka amince dashi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel