Bayan Ta Karbi Haya, Budurwa Ta Zage Ta Yi Fentin Gidan Tare Da 'Kawata Shi da Kanta

Bayan Ta Karbi Haya, Budurwa Ta Zage Ta Yi Fentin Gidan Tare Da 'Kawata Shi da Kanta

  • Wata matashiya yar Najeriya wacce ta rasa kudin daukar mai fentin da zai yi mata a gida ta yanke shawarar zagewa ta yi abunta da kanta
  • Bayan ta siya roban fenti kanana guda biyu kan N2,000 kowanne, sai ta zuba wani sinadarin kyalli a ciki don gwada sa'arta
  • Mutane da dama da suka ga yadda ta yi fentin daki da falonta ba tare da ta biya wani ya yi mata ba sun yi mata tambayoyi

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna @beautynain, ta garzaya shafin soshiyal midiya don wallafa wani bidiyo na yadda ta sauya gidan da ta karba haya duk da cewar bata da kudi.

Ganin cewa bata da kudin yiwa gidan fenti da biyan mai fenti, sai matashiyar wacce ta bayyana kanta a matsayin "mai cin gashin kanta" ta siya kyalli sannan ta hada su a wasu kananan roban fenti biyu da ta siya kan N2,000 kowanne.

Kara karanta wannan

Kyakyawar Baturiya Ta Tafi Da Saurayinta Dan Najeriya Kasarsu Don Ya Gana Da Danginta, Bidiyon Ya Kayatar

Budurwa da fenti
Bayan Ta Karbi Haya, Budurwa Ta Zage Ta Yi Fentin Gidan Tare Da Kawata Shi da Kanta Hoto: TikTok/@beautynain
Asali: UGC

Matashiya ta yi aiki da tsarin yi kai wajen fentin gidanta

A yayin daukar bidiyon, ta bayyana cewa yayin da ta kai wani mataki, abun ya ishe ta saboda ya bata mata gashinta da wurare daban-daban na dakin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tana da kawa mace wacce ta zo tayata da aikin fenti. Ta yi fentin cikin dakinta kala daban da wanda ta yi amfani da shi a Falo. Mutane da dama sun kayatu da sakamakon nasarar da ta samu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

ogemark ta ce:

"Menene manufar kyallin."

Zita ta tambaya:

"A ina kika samu fentin 2k dan Allah? Ina so na zo na siye dukka."

Ta amsa:

"A Ketu na siya, koda yake karami ne."

Emmabest Eyo ta ce:

"Kin karfafa mani gwiwar yin nawa da kaina. Lagas kike da zama."

Kara karanta wannan

Yadda Hannun Gajeruwar Yar Bautar Kasa Ya Gaza Kaiwa Saman Allo, Dalibai Sun Fashe Da Dariya a Bidiyo

Ruqoyah ta ce:

"Da kin watsa kyallin a jikin bangon bayan kin gama fentin maimakon zuba shi a cikin fentin, zai fito da kyau."

Matashi ya kera motar wasan tsere da hannunsa a Najeriya

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya sha jinjina a soshiyal midiya sakamakon kera wata motar wasan tsere da ya yi da kansa.

Mutane sun kayatu matuka yayin da suka ci karo da bidiyon matashin yana tuka motar tasa a garin Edo, babban birnin jihar Benin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel