A Kokarin Wanke Obasanjo, Jagora a APC Ya ba Atiku Kariya a Rigimarsa da Ministan Tinubu

A Kokarin Wanke Obasanjo, Jagora a APC Ya ba Atiku Kariya a Rigimarsa da Ministan Tinubu

  • Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode ya kare mulkin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar
  • Ya ce Obasanjo ya gaji kamfanin sufurin jiragen sama cikin mawuyacin hali a 1999, bayan almundahana da rashin shugabanci
  • Fani-Kayode ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta tarayya ta ƙi amincewa da bukatarsa ta biyan fansho a 2006

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Femi Fani-Kayode, jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, ya kare tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo da aka yi zargi da kashe wani kamfani.

Fani-Kayode ya yi martani ne kan rugujewar kamfanin jiragen sama na Nigeria Airways, yana mai cewa ba shi ne ya jawo matsalar da ta dabaibaye kamfanin ba.

Na kusa da Tinubu ya kare Obasanjo
Shugaba Bola Tinubu da Olusegun Obasanjo. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Fani-Kayode ya mayar da martani ne ga kalaman Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci Gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo wanda ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Abin da Tinubu ya faɗa wa taron ƴan tsintsiya kan shirin kamfen

Abin da Keyamo ya ce ga Obasanjo

Keyamo ya ce Shugaba Bola Tinubu yana biyan basussukan fansho da alawus-alawus da ake bin tsofaffin ma’aikatan Nigeria Airways tun bayan rushe kamfanin a watan Satumban 2004.

Keyamo ya zargi gwamnatin Obasanjo, wadda Atiku Abubakar ya yi mata mataimakin shugaban ƙasa, da rushe kamfanin jiragen saman ƙasa tare da barin dubban ma’aikata ba tare da fansho da alawus-alawus ba.

Martanin Fani-Kayode ga Keyamo

Sai dai Fani-Kayode, wanda shi ma ya taɓa zama ministan sufurin jiragen sama a lokacin gwamnatin Obasanjo, ya ce Obasanjo ya gaji kamfanin cikin mawuyacin hali, inda jirgi guda ɗaya kacal ya rage, kuma ba ya aiki, lokacin da ya koma mulki a matsayin shugaban ƙasa farar hula.

Jakadan ya ce:

“Don yin adalci ga Shugaba Obasanjo, matsalar Nigeria Airways, kamar yadda ka bayyana ta, ta samo asali ne tun kafin ya dawo kan mulki a shekarar 1999.

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

“Lallai kamfanin yana cikin mawuyacin hali, amma ba Obasanjo ne ya jawo hakan ba. Ya same shi a wannan yanayi bayan an rantsar da shi, kuma abin da ya gani ya karya masa zuciya.”
Jigo a APC ya ba Obasanjo kariya da aka zargi gwamnatinsa
Tsohon minista kuma jakada a gwamnatin Bola Tinubu, Femi Fani-Kayode. Hoto: Femi Fani-Kayode.
Source: Facebook

Karin haske da Fani-Kayode ya yi

Tsohon ministan ya ce lokacin da Obasanjo ya bar mulki a matsayin shugaban ƙasa na soja a shekarar 1979, Nigeria Airways tana da jirage 32 masu aiki, ƙwararrun matukan jirgi da ma’aikata, ƙwararrun shugabanni da kuma kwamitin gudanarwa mai bin ƙa’ida.

Sai dai ya ce zuwa shekarar 1999, kusan dukkan kadarorin kamfanin sun ɓace, ayyukansa sun lalace, kuma ya faɗa cikin matsanancin basussuka.

Fani-Kayode ya danganta rugujewar kamfanin tsakanin shekarun 1979 da 1999 da cin hanci da rashawa da kuma rashin kyakkyawan shugabanci daga shugabannin gudanarwa da kwamitocin da suka jagoranci kamfanin a lokuta daban-daban.

Ya ce:

"An kammala aikin rufe kamfanin bisa doka a shekarar 2004.
“An yanke wannan shawara ne bayan shekaru na tabarbarewa da yunƙurin farfaɗo da kamfanin da suka gaza, ciki har da shawarar Hukumar Kuɗi ta Duniya (IFC) kan sayar da kamfanin ga masu zaman kansu, wadda daga baya ta janye."

Kara karanta wannan

Wai Trump ya nemi afuwar Tinubu kan wasu zarge zarge? Ga abin da aka binciko

Dalilin neman barin Turai zuwa Afirka - Fani-Kayode

A baya, an ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya tabbatar da nadinsa a matsayin jakadan Najeriya zuwa Afirka ta Kudu.

Fani-Kayode wanda tsohon 'dan PDP ne ya ce hakan ya faru ne bayan amincewar Bola Tinubu saboda korafin da ya yi ga shugaban kasa.

Ya ce shi ne ya nemi a mayar da shi Afirka ta Kudu zuwa Jamus saboda ra'ayinsa na ɗan Afirka da kusancin manufofin ƙasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.