Manyan Yan Sanda Sun Shiga Matsala bayan Yan Kungiyar Asiri Sun Gyara Caji Ofis

Manyan Yan Sanda Sun Shiga Matsala bayan Yan Kungiyar Asiri Sun Gyara Caji Ofis

  • Rundunar ’yan sandan Rivers ta dakatar da jami’an DPO biyu bayan zargin wasu ’yan ƙungiyar asiri sun gyara ofishinta
  • Kakakin rundunar ya ce an fara bincike domin gano waɗanda suka ɗauki nauyin gyaran, jami’an da suka amince da aikin
  • Kwamishinan ’yan sandan Rivers, Olugbenga Adepoju, ya ba da umarnin gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Rundunar ’yan sandan jihar Rivers ta ce ta dakatar da jami’ai biyu daga aikinsu na wucin gadi.

Hakan ya faru yayin da ake bincike kan zargin wasu ’yan ƙungiyar asiri sun gyara ofishin ’yan sanda na Abuloma.

An dakatar da yan sanda 2 a Rivers
Sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Jami’an da abin ya shafa su ne babban jami’in ’yan sanda mai kula da sashen Abuloma, wato DPO, da jami’in da ke kula da ofishin ’yan sandan da aka gyara, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

An rasa malamin addini sama ko ƙasa yayin komawa gida, ƴan bindiga sun ɗauke shi

Yan sanda sun yi Allah-wadai da lamarin

Agabe Kaborlo, kakakin rundunar, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, bayan rahotanni da wani bidiyo kan lamarin sun bazu a kafafen sada zumunta.

Rundunar ta ce tana yin Allah-wadai da duk wani aiki ko alaƙa da za ta iya lalata mutunci, ladabi da ƙwarewar aikin rundunar ’yan sandan Najeriya.

Sanarwar ta ce:

“Ba za a amince da duk wani abu da zai ba ƙungiyoyin asiri da ake zargi ko wasu ƙungiyoyin haramtattu martaba, karɓuwa ko halaccin gudanar da ayyukansu ba.
“Ofisoshin ’yan sanda cibiyoyi ne na jama’a da aka kafa domin kare ’yan ƙasa da tabbatar da bin doka, don haka bai kamata su zama wuraren da ƙungiyoyin masu laifi ke neman karɓuwa ko tasiri a cikin al’umma ba.”
Maganganu sun biyo bayan gyara ofishin yan sanda da kungiyar asiri ta yi
Taswirar jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

An dakatar da DPO a Rivers

Saboda haka, an aika wa DPO na sashen Abuloma da jami’in da ke kula da ofishin takardar neman bayani, tare da cire su daga mukamansu yayin da ake gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da ke guduwa zuwa Zamfara sun tsaya a hanya, sun yi barna a Niger

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Olugbenga Adepoju, ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano yadda lamarin ya faru da kuma tabbatar da gaskiyar zarge-zargen.

Sanarwar ta ce binciken zai gano mutanen da suka ba da kuɗi ko taimaka wajen gyaran, jami’an da suka amince da aikin, ko an bi ƙa’idojin da suka dace, da kuma ko wani jami’in ’yan sanda ya karya ƙa’idojin aikinsa.

Rundunar ta bayyana cewa ofisoshin ’yan sanda cibiyoyin jama’a ne da aka kafa domin kare al’umma da tabbatar da bin doka, ba wuraren da masu laifi kamar yan kungiyar asiri za su nemi karɓuwa ba.

Ta kuma bayyana cewa jama’a na iya bayar da gudummawa bisa doka domin inganta ofisoshin ’yan sanda, kamar yadda sashe na 26(1)(d) na dokar ’yan sandan Najeriya ta 2020 ya tanada.

Sai dai sanarwar ta jaddada cewa irin wannan taimako bai kamata ya shafi ’yancin gudanar da aikin ’yan sanda, ƙa’idojin sana’ar ko tsaro ba, cewar Vanguard.

Kungiyar asiri: Yan sanda sun cafke saniya

A baya, mun ruwaito muku cewa ‘yan sanda sun kama wata saniya tare da tafiya da ita bayan kokarin kama wasu ‘yan kungiyar asiri a jihar Osun.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da wasu ‘yan kungiyar asiri suka shirya yin wani katafaren biki a jihar kafin asirinsu ya tonu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.