Tinubu Ya Gana da Hafsoshin Tsaro kan 2027, Ya Aika Sako ga Atiku da Sauransu

Tinubu Ya Gana da Hafsoshin Tsaro kan 2027, Ya Aika Sako ga Atiku da Sauransu

  • Shugaba Bola Tinubu ya gana da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa a ranar Alhamis, inda ya ba su umarnin ruguza dukkan sansanonin 'yan ta'adda
  • A bayanan da Legit Hausa ta samu, shugaban kasar ya ba jami'an tsaron Najeriya umarnin ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar
  • Taron wanda ya ɗauki tsawon sa'o'i da dama, ya kuma maida hankali ne kan hanyoyin samar da yanayi mai kyau domin gudanar da zaɓen shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya gana da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya ba su umarnin gaggawa na zakulo tsagerun 'yan bindiga da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a duk inda suke.

Kara karanta wannan

An hura wa Tinubu wuta kan 2027, ana so ya hakura da shiga takara

Ministan Tsaro, Christopher Musa ya bayyana cewa sun je fadar shugaban ƙasa ne domin yi wa Shugaban Ƙasar bayani kan halin tsaro na ƙasar, sannan da nuna muhimmancin kiyaye tsaro yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa ministan tsaron ya tabbatar da cewa taron ya sami halartar dukkan shugabannin hukumomin tsaro, kuma Tinubu ya ba su umarnin share dukkan sansanonin 'yan ta'adda da 'yan bindiga a ƙasar.

Sakon Tinubu ga 'yan adawa

Janar Musa ya bayyana cewa tattaunawar ta kasance mai zurfi, inda Shugaba Tinubu ya jaddadawa 'yan adawa da jama'a kasa cewa yana son a gudanar da zaɓe na gaskiya.

Daily Trust ta rahoto ya ce:

"Muna bukatar yin dukkan mai yiwuwa domin tabbatar da cewa ƙasar tana da aminci da tsaro ga 'yan ƙasa domin su fito su ƙaɗa ƙuri'arsu. Don haka muna son tabbatar wa 'yan Najeriya cewa muna aiki tuƙuru domin samar da tsaro ga kowa."

Ministan ya ƙara da cewa rundunonin tsaro za su kasance tsakatsaki babu ruwansu da jam'iyyar siyasa, inda za su ba kowa damar fitowa ba tare da tsoron tsangwama ko firgiti daga kowa ba.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun maida martani da Tinubu ya ce ba zai iya zuwa kamfe wasu jihohi ba

Batun jin dadin jami'ai

Haka zalika, ya jaddada cewa gwamnati tana inganta jin dadin jami'an tsaro ta hanyar ƙara musu albashi, horo, da kawo sababbin kayan aiki.

"A kwanan nan Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da sababbin jiragen sama da na helikopta da aka saya, waɗanda yawansu ya kai kusan guda 10, domin nuna wa 'yan Najeriya cewa duk da matsalolin tattalin arziƙi, tsaron ƙasar yana da muhimmanci.
"Shugaban ƙasa yana son kowane ɗan Najeriya ya kasance cikin farin ciki da abubuwan da ke faruwa, kuma muna neman haɗin kan 'yan ƙasa domin tabbatar da cewa Najeriya ta tsira."
Hafsoshin tsaron Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu da hafsoshin tsaro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shekarau ya yabi Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa manyan shugabannin siyasa da jiga-jigai daga shiyyar Arewa sun bayyana goyon bayansu a hukumance ga aniyar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Tawagar, wadda ta ƙunshi masu ruwa da tsaki daga shiyyoyin Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Gabas, ta bayyana wannan mataki ne bayan ganawa da Kashim Shettima.

Yayin da yake jawabi a madadin ƙungiyar, tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Ibrahim Shekarau, ya ce za su kawowa Bola Tinubu Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng