Akwai Dalili: Me Yasa Gwamnoni 33 ke Goyon Bayan Tazarcen Tinibu?
- Hadimin shugaban kasa a Najeriya ya ce gwamnonin jihohi 33 ba za su yi kuskure ba wajen goyon bayan Tinubu
- Bayo Onanuga ya ce farashin kayan abinci ya ragu, ajiyar kuɗin ƙasashen waje ta ƙaru, sannan ’yan Najeriya sun fara amfani da katunan bankinsu ƙasashen waje
- Ya kuma ce masu zuba jari na ƙasashen waje sun dawo Najeriya, suna kawo kuɗaɗe da samar da ayyukan yi, duk da sukar da ake yi wa tattalin arzikin ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara ta musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya yi magana kan salon mulkin Bola Tinubu.
Onanuga ya kare nasarorin tattalin arzikin gwamnatin shugaban ƙasar, inda ya bayyana cewa gwamnonin jihohi 33 ba za su yi kuskure ba wajen goyon bayan gwamnatinsa.

Source: Twitter
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a.
Onanuga ya kuma ambaci raguwar farashin kayan abinci, ƙaruwar ajiyar kuɗin ƙasashen waje, ingantaccen samun kuɗaɗen waje da kuma dawowar masu zuba jari a matsayin alamun ci gaba ƙarƙashin mulkin Tinubu, wanda ya hau mulki a watan Mayun 2023.
Ya soki masu gabatar da shirye-shiryen talabijin bisa tambayar da suke yi kan ci gaban tattalin arzikin ƙasar, yana zarginsu da yaɗa ra’ayin ’yan adawa na cewa babu wani ci gaba mai ma’ana tun bayan da Tinubu ya zama shugaban ƙasa.
Onanuga ya ce:
“Masu gabatar da shirye-shiryen talabijin suna ci gaba da yaɗa ra’ayin ’yan adawa cewa babu wani abu mai kyau da ya canza tun shekarar 2023, alhali kuwa an samu gagarumin ci gaba. Ra’ayinsu ya zama abin dariya, har suna ci gaba da maimaita tsohon zance, kuma yanzu suna tambayar sahihancin bayanan Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) kan raguwar hauhawar farashin kayayyaki. Zan ba su shawarar su koma kasuwanni su gani da kansu.”
Ya ce farashin buhun shinkafa ya ragu daga kusan N120,000 zuwa ƙasa da N50,000, yana mai cewa a garinsu ana sayar da buhu ɗaya kan N45,000.
Onanuga ya bayyana cewa:
"Shinkafar da aka saba so, wadda a wani lokaci ake sayar da buhunta kan N120,000, yanzu farashinta ya faɗi ƙasa da N50,000. A garina, ana sayar da buhu ɗaya kan N45,000.”
Mataimakin shugaban ƙasar ya yi iƙirarin cewa rahotannin raguwar farashin kayan abinci da hauhawar farashin kayayyaki sun nuna cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Ya buƙaci masu gabatar da shirye-shiryen talabijin da ke tambayar sahihancin alkaluman da aka fitar da su je kasuwanni domin tantance farashin kayayyakin da ake sayarwa.
Onanuga ya kuma yi nuni da ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Najeriya da kuma damar da ’yan Najeriya suka samu na amfani da katunan bankinsu masu ɗauke da kuɗin naira a ƙasashen waje a matsayin alamun ingantuwar tattalin arzikin ƙasar.
Ya ce:
"Ajiyar kuɗaɗen ƙasarmu ta kusa kai dala biliyan 60. Yanzu ’yan Najeriya na iya amfani da katunan bankinsu na naira a ƙasashen waje, abin da ba zai yiwu ba kafin Tinubu ya zama shugaban ƙasa.”

Kara karanta wannan
"Sun tsorata," Kwankwaso ya gano sasu shirin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Ya ƙara da cewa ’yan kasuwa yanzu suna iya samun kuɗaɗen waje domin shigo da albarkatun ƙasa da kayan aiki, abin da ya ce zai taimaka wa harkokin kasuwanci da bunƙasa ayyukan tattalin arziki.
Tinubu ya naɗa sababbin Kwamishinonin INEC
An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya naɗa sababbin kwamishinonin shida a hukumar zabe mai zaman kanta, INEC yayin da ke tunkarar zaben 2027.
Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai Farfesa Mustapha Aliu da Bashir Muhammed Umar, waɗanda za su wakilci Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance waɗanda aka naɗa gabanin babban zaɓen da za a gudanar a watan Janairu mai zuwa.
Asali: Legit.ng

