Bidiyon Yarinya da ta Girma a Cikin Karnuka 5, Tana Rayuwa da Tafiyar Yadda Suke yi

Bidiyon Yarinya da ta Girma a Cikin Karnuka 5, Tana Rayuwa da Tafiyar Yadda Suke yi

  • Wata 'yar karamar yarinya da ta tashi cikin manyan karnuka 5 ta tsinci kanta tana rayuwa kamar dabbobin rainonta tare da gwada cin abincinsu
  • Mahaifiyar yarinyar ce ta wallafa bidiyon yarinyar a TikTok tare da kwatantata da Mowgli na Legend of the Jungle
  • Masu amfani da kafar TikTok da dama sun cika da mamakin ganin bidiyon wanda a yanzu haka sama da mutane 2.0 miliyan suka kalla da jinjina sama da 541,900

Wata 'yar karamar yarinya mai ban sha'awa, wacce ta taso cikin karnuka biyar yanzu ta koma rayuwa kamar dabbobin rainonta.

A wani bidiyo da ke bayyana yadda yarinyar ke rayuwa da @von.jakoba ta wallafa a TikTok, wacce ta kwatantata da Mowgli na fim din Legend of the Jungle.

Baby mai rayuwa cikin kare
Bidiyon Jinjirin da ya Girma a Cikin Karnuka 5, Yana Rayuwa da Tafiyar Yadda Suke yi. Hoto daga TikTok/@von.jakoba
Asali: UGC

Faifan bidiyon da ya fara da yadda karnukan ke kula gami da rainon yarinyar lokacin da bata kai haka tasawa ba.

Kara karanta wannan

Jami'an Tsaron Nigeria Sun Sanar Da Halaka Yan Ta'adda Kusan 50, Kuma Sun Kama 62

A dayan bidiyon, an ga yadda aka haifi yarinyar cikin karnuka, ta zauna tana rike da robar ruwan karen tare da saka hannunta na hagu ciki kamar tana so ta sha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika, an ga yadda jinjirar ke rarrafe da kafa hudu kamar 'dan kuikuyo. Maimakon amfani da hannayenta, ta yi amfani da bakinta wajen kama 'yar bebinta yadda kare ke yi.

A bidiyon na karshe, ta yi rarrafe da hudunta gami da haduwa da wani bakin kare cikin wani karamin tafki. Baya ga rayuwar da take kamar 'dan kuikuyo, yarinyar na kwatanta cin abincin kare wanda a yanzu sama da mutane 2.9 miliyan suka kalla.

Martanin jama'a

@Shep ya ce:

"Wannan ita ce jinjirar da za ta fada da gaske damisoshi ne suka raineta."

Kara karanta wannan

Ina Biyan Kudin Haya N800k Duk Shekara: Budurwa Ta Nuna Cikin Dakinta Da ke Da Wuta 24/7

@Allison Bruveris yayi martani:

"Za ta zama mai garkuwar jiki mai karfi! A tunanina hakan na da ban sha'awa!

@Sarah Nichole ta ce:

"Muna da karnuka hudu."

@Theresabbb tayi martani:

"Tayaaaa zan iya son wannan fiye da so daya!!! Kin hadu!"

Lakadata yake kamar jaka, Matar Aure ga kotu

A wani labari na daban, wata matar aure ta tsaya a gaban kotu inda ta nemi a tsinke igiyar aurenta da mijinta mai shekaru 8 kuma ya samar da yara biyu.

Ta sanar da yadda mijin yake cin zarafinta tare da dukanta sannan ba ya daukar dawainiyarta baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel