Wani Mutum Ya Jero Sharudda, Yana Neman Mata Ta Biyu, Zai Ba Ta Sadaki N1m da Karin N200k

Wani Mutum Ya Jero Sharudda, Yana Neman Mata Ta Biyu, Zai Ba Ta Sadaki N1m da Karin N200k

  • Wani mutum dan jihar Kaduna ya bayyana kadan daga abin da yake bukata na auren mata ta biyum ya fada cikiya
  • A cewarsa, zai ba da sadakin N1m, mma ba zai ba da lefe ba, kuma ba ya bukatar matar ta zo masa da kayan daki
  • Hakazalika, ya ce babu batun dauke-dauken hotuna kafin biki da dai sauran bukukuwan bidi'a da basu da ma'ana

Najeriya - Wani mutum mai shekaru 49 dan jihar Kaduna ya bayyana cewa, yana neman mata ta biyu zai aura, zai yi mata gatan da ba a saba gani ba.

Mutumin ya ba da cikiyar neman auren a wani shafin Twitter mai suna Halal Matchmaking a ranar Alhamis 12 ga watan Janairun 2023.

Shafin na Halal matchmaking dai wata kafa ce fitacciya da ta yi shuhura wajen nemawa Musulmai aure ba tare da wata matsala ba, kuma shafin kan nuna irin nasarorin da ya samu.

Kara karanta wannan

2023: Kada Ku Mika Kasa Mai Lalura Ga Mutumin Da Bai Da Lafiya, Peter Obi Ga Yan Najeriya

Mutum mai neman aure a Twitter
Wani Mutum Ya Jero Sharudda, Yana Neman Mata Ta Biyu, Zai Ba Ta Sadaki N1m da Karin N200k | Hoto: @Halal_Match
Asali: Twitter

Batun mai neman karin aure

A bayanin da aka yada, mutumin ya bayyana sharuddan da yake so matarsa ta biyu ta cika, kana zai ba da sadaki mai tsoka da kuma diyyar hana amaryar tasa yin wasu bukukuwan bidi'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar sanarwar da Halal ta yada, mutumin yana neman bazawara mai shekaru tsakanin 30-35, ba 'yar lukuta ba, mai addini, Bahaushiya ko Bafulatana, ko Kanuri ko mai dai Bayarbiya.

Hakazalika, ya ce ba zai yi kayan lefe ba, kuma ba ya bukatar sai amaryar ta zo da kayan daki balle na madafa.

A madadin lefe, ya ce zai ba ta miliyan 1 a matsayin sadaki, kana ya hana ta daukar hotunan kafin biki da kuma yin wani taron 'dinner' balle 'party'.

A bangarensa, ya ce zai ba ta diyyar N200,000 saboda rage mata radadin tarukan bidi'a da za a yi a bikin.

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

Meye sahihancin shafin Halal Match Making?

Legit.ng Hausa ta yi duba ga shafin na Twitter, inda ta ga ikrarin shafin na hada aure cikin nasara har sau sama da 70.

Hakazalika, mun yi duba ga shafin rajistar kamfanoni da kungiyoyi ta Najeriya, CAC don bincika ikrarin Halal Match Making cewa tana da rajista tare da bayyana lambar CAC.

Mun gano kamfanin na kan yin rajista da CAC a matsayin kamfani, amma har yanzu rajistan bai kammala ba.

Mai neman aure a Twitter
Wani Mutum Ya Jero Sharudda, Yana Neman Mata Ta Biyu, Zai Ba Ta Sadaki N1m da Karin N200k | Hoto: search.cac.gov.ng
Asali: UGC

Aure babban nasara ne

A wani labarin kuma, wata mata ta bayyana cewa, aure ne babban nasara ce a rayuwarta, kuma ba za ta taba mantawa ba.

Ta ce a lokacin da take waje bata yi aure ba, ta ga tsiyar hali da mutane ke yi mata, ta ce yanzu ta tsallake komai.

Ta ce a yanzu dai ta fi karfin zagi, domin sunanta matar wani kuma mai daraja ta igiyar aure.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Matshi Da Yaje Ba Haya A Dawa Karke Da Fada Da Damisa Wadda Ta Jikkatashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel