Oyebanji Ya Kafa Tarihi da Aka Rantsar da Shi a Matsayin Gwamna Karo na 2 a Najeriya
- An rantsar da gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji karo na biyu bayan nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar a shekarar 2026
- Gwamna Biodun Oyebanji ya zama gwamna na farko a tarihin Ekiti da ya samu damar yin wa’adi biyu a jere
- Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wajen bikin rantsuwar yau Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ekiti, Nigeria - Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya karbi rantsuwar kama aiki a wa’adin mulki karo na biyu a ranar Juma’a, 16 ga watan Oktoba, 2026.
Hakan ya sa Gwamna Oyebanji ya zama gwamna na farko a tarihin jihar Ekiti da ya sake lashe zaɓe domin ci gaba da mulki na wa’adi biyu a jere.

Source: Facebook
An rantsar da gwamnan jihar Ekiti

Kara karanta wannan
Wajen rantsar da kwamitin kamfe ya zama matattarar habaici tsakanin Akpabio, Wike da gwamnoni
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an rantsar da Oyebanji tare da mataimakiyarsa, Cif Monisade Afuye, a dandalin Ekiti Parapo da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar.
Babban Alƙalin jihar Ekiti, Mai Shari’a Lekan Ogunmoye, ne ya jagoranci bikin rantsarwar.
Oyebanji ya karanta rantsuwar kama aiki da ta biyayya da ƙarfe 1:40 na rana, a gaban dimbin manyan baki, shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya da magoya bayansa da suka halarci wurin domin shaida wannan muhimmin lamari.
Daga bisani, ya sanya hannu kan takardun da suka wajaba domin tabbatar da kama wa’adin mulkinsa na shekaru huɗu na biyu.
Tun da farko, Afuye ta karanta rantsuwar kama aiki da ta biyayya da ƙarfe 1:28 na rana, sannan ta sanya hannu kan takardun da suka dace, cewar rahoton Vanguard.
Sake zaɓen Oyebanji da rantsar da shi sun zama wani muhimmin tarihi a siyasar jihar Ekiti, domin ya karya abin da ake gani a matsayin ƙalubalen sake samun wa’adi a jere, bayan gwamnatocin baya sun kasa samun nasarar ci gaba da mulki na wa’adi na biyu.
Manyan baki sun halarci bikin
Bikin ya samu halartar manyan shugabannin siyasa, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilta.
Haka zalika, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau; da Ministan Ma’adinai da Ƙarafa, Dele Alake na cikin wadanda suka halarta.

Source: Facebook
Gwamnoni da wakilan gwamnatocin jihohi ma sun halarci taron, tare da tsofaffin gwamnoni a jihar Ekiti, Ayodele Fayose, Segun Oni da Kayode Fayemi, da shugabannin jam’iyyar APC, sarakunan gargajiya da sauran manyan baki.
Daga cikin gwamnonin da suka halarta akwai Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan Imo, Hope Uzodinma; Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, tare da wakilan sauran gwamnatocin jihohi.
Oyebanji ya roki musulmin Ekiti
Kun ji cewa gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya roƙi Musulman jihar su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Oyebanji ya kuma tabbatar wa al’ummar Musulmi cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsarin mulki mai bai wa kowa dama, ba tare da nuna bambanci ba.
Asali: Legit.ng
