An Rasa Malamin Addini Sama ko Ƙasa yayin Komawa Gida, Ƴan Bindiga Sun Ɗauke Shi
- Rundunar ’yan sandan Benue ta tabbatar da sace wani limamin cocin Katolika a ƙaramar hukumar Ohimini ta jihar
- Cocin Katolika ta Otukpo ta ce an sace limamin ne ranar 13 ga Oktoba, yayin da yake komawa gida daga Otukpo ta hanyar Otobi Amejo-Ajegbe
- ’Yan sanda sun fara bincike domin ceto limamin, yayin da cocin ta buƙaci limamai da sauran al’umma su yi addu’ar samun kuɓutarsa cikin ƙoshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Rundunar ’yan sandan jihar Benue ta yi magana kan rahoton sace wani babban fasto a jihar.
Yan sandan sun tabbatar da sace Rabaran John Otache, limamin cocin St. Margaret da ke Ajegbe-Awume, a ƙaramar hukumar Ohimini ta jihar.

Source: Twitter
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, DSP Aondogu Orchia, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Juma’a a Makurdi, cewar Punch.
Orchia ya ce rundunar ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da limamin wanda ya tayar wa al'ummar yankin hankali matuka.
Yadda aka sace fasto a Benue
A wani rahoto makamancin haka, cocin Katolika ta Otukpo ta bayyana cewa an sace limamin ne ranar 13 ga Oktobar shekarar 2026.
A cikin wata sanarwa da shugaban gudanarwar cocin Katolika ta Otukpo, Rabaran Joseph Itodo, ya sanya wa hannu, ya bayyana yadda lamarin ya faru.
A cewarsa, Otache yana komawa gida daga Otukpo ne lokacin da ya ci karo da masu garkuwa da mutane a kan hanyar Otobi Amejo-Ajegbe, da ke ƙaramar hukumar Ohimini ta jihar Benue.

Source: Original
Coci ta yi allah-wadai da sace limamin
Itodo ya bayyana alhininsa kan lamarin, inda ya ce Bishop na Otukpo, Most Rev. Michael Apochi, ya nuna matuƙar damuwa da abin da ya faru, cewar Vanguard.
Ya yi kira ga limamai, masu gudanar da ayyukan addini, mabiya cocin da sauran masu kishin al’umma da su yi addu’ar ganin an saki limamin cikin ƙoshin lafiya ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma, ya buƙaci a yi addu’a ga sauran mutanen da masu garkuwa da mutane ke riƙe da su a sassa daban-daban na Najeriya, yana mai fatan za su koma ga iyalansu lafiya.
Ya bayyana cewa:
Otache yana komawa gida ne daga Otukpo lokacin da ya ci karo da masu garkuwa da mutane a kan hanyar Otobi Amejo-Ajegbe, da ke ƙaramar hukumar Ohimini.
Yan bindiga sun yi barna a Benue
Mun ba ku labarin cewa yan bindiga da ake zargin Fulani Makiyaya ne sun kai sababbin hare-hare kan wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Ukum ta Jihar Benue.
Wani mazaunin yankin ya ce an kashe mutum tara, amma an gano gawarwaki shida kacal a lokacin haɗa wannan rahoton.
Wata majiya mai tushe a ɓangaren tsaro ta ce har yanzu ba a ga wasu mazauna yankin ba bayan hare-haren.
Asali: Legit.ng

