Gwamna Ya Saya wa Dubban Matalautan Mata Hannun Jarin Matatar Dangote

Gwamna Ya Saya wa Dubban Matalautan Mata Hannun Jarin Matatar Dangote

  • Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ware miliyoyin Naira domin sayen hannayen jari a matatar Dangote ga mata
  • Gwamnatin Gombe da gidauniyar Aliko Dangote za su bai wa kowace mace hannayen jari 20 domin inganta tattalin arzikinta da rage talauci
  • Gidauniyar Aliko Dangote ta yaba masa bisa kasancewarsa gwamna na farko da ya shirya tallafa wa mata masu ƙaramin ƙarfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ware N149,224,806 domin taimakawa mata marasa galihu a jihar.

Gwamnan ya amince da sayen hannayen jari a matatar Dangote ga mata 28,284 masu rauni a faɗin jihar.

Gwamna ya ware miliyoyi domin saya wa mata hannun jari a matatar Dangote
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya yayin taro a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya wallafa a Facebook a ranar Alhamis.

Dalilin sayan hannun jari ga mabukatan mata

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Must Go, ƴan APC sun bullo da Tinubu Must Go Again a Adamawa

Sanarwar ta bayyana cewa kuɗin wani ɓangare ne na gudummawar da jihar za ta bayar bisa yarjejeniyar haɗin gwiwa da Gidauniyar Aliko Dangote (ADF), domin mata masu ƙaramin ƙarfi su amfana da shirin ƙarfafa tattalin arziki.

Ya ce Gwamna Yahaya ya amince da gudummawar jihar ga shirin, wanda ya shafi ƙananan hukumomi 11 na jihar, da nufin inganta shigar mutane cikin harkokin kuɗi, samar da arziki da kuma rage talauci mai ɗorewa.

A cewarsa, bisa tsarin shirin, gudummawar gwamnatin jihar za ta samar da hannayen jari 10 ga kowace mace da za ta amfana, yayin da Gidauniyar Aliko Dangote za ta ƙara wasu 10, wanda zai kai jimillar hannayen jari 20 ga kowace mace.

An tsara shirin ne domin bai wa mata masu rauni damar mallakar kadarorin kuɗi, ƙarfafa juriyarsu ta fuskar tattalin arziki da kuma samar musu da damar inganta rayuwarsu da samun 'yancin dogaro da kansu ta fuskar kuɗi.

Ana ci gaba da sayan hannun jarin Dangote
Shugaban kamfanin matatar Dangote, Alio Dangote. Hoto: Dangote Foundation.
Source: Facebook

Abin da Gidauniyar Dangote ta ce

Da take magana kan haɗin gwiwar, shugabar Gidauniyar Aliko Dangote, Zouera Yusuf, ta yaba wa Gwamna Yahaya bisa kasancewarsa gwamna na farko a Najeriya da ya shiga shirin tare da cika sharadin bayar da gudummawar da ake buƙata.

Kara karanta wannan

An kai ɗan Najeriya kotu kan ikirarin mallaka da shirin cefanar da jirgin sojoji

Ta amince da ƙudirin gwamnatin jihar na ƙarfafa mata ta hanyar tsare-tsare da shirye-shiryen da aka tsara domin inganta jin daɗin ƙungiyoyin da ke cikin mawuyacin hali.

Zouera ta bayyana cewa haɗin gwiwar zai ƙara samar da damammakin tattalin arziki ga mata da iyalansu.

Misilli ya ƙara da cewa, domin tabbatar da ingantaccen haɗin kai, aiwatar da shirin cikin gaskiya da kuma riƙon amana, gwamnatin jihar ta ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwa tsakanin sassa daban-daban domin kula da yarjejeniyar da tabbatar da nasarar shirin.

Sanarwar ta ce:

“Kwamitin ya ƙunshi wakilan Ma'aikatar Kuɗi da Ci gaban Tattalin Arziki, Ma'aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Al'umma, da kuma Ma'aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci.”

Gwamnan Kwara zai saya malamai hannun jari

An ji cewa Gwamnatin Kwara ta shirya sayen hannun jarin matatar Dangote ga mata malamai, domin karfafa musu guiwa.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce za a bai wa mata malamai hannun jari 10,000, tare da shirin fadada tsarin.

Gwamnatin ta kuma ware N120m ga fitattun malamai, shugabannin makarantu da jami’an ilimi domin yaba kokarinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.