Takarar Pantami da hadu da sabon kalubale daga babban dan PDP

Takarar Pantami da hadu da sabon kalubale daga babban dan PDP

  • Wani mai neman tikitin PDP a Gombe, Usman Aliyu Garry, ya shigar da ƙorafi ga INEC kan cancantar jam’iyyar ta tsayar da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami takarar gwamna a 2027
  • Garry ya nemi INEC ta binciki kundin rajistar mambobin PDP a jihar, domin tabbatar da ko jam’iyyar ta bi ƙa’idojin dokar zaɓe wajen rajistar mambobinta da tsayar da ɗan takara
  • Ƙorafin ya ƙara tsananta takaddamar siyasa da ta shari’a da ke tattare da zaɓen ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe gabanin babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Takaddamar shari’a kan ɗan takarar gwamnan Gombe na jam’iyyar PDP a zaɓen 2027 ta sake ɗaukar sabon salo, bayan da ɗaya daga cikin masu neman tikitin jam’iyyar, Usman Aliyu Garry, ya shigar da ƙorafi ga INEC.

Kara karanta wannan

Tawagar Tinubu ta tafi neman addu'a fadar manyan sarakuna a Najeriya

A cikin wasiƙar da ya aikawa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, Garry ya yi zargin cewa akwai matsaloli a kundin rajistar mambobin PDP da kuma yadda jam’iyyar ta bi tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami a Najeriya. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Korafin Garry kan Pantami

Daily Trust ta wallafa cewa wasiƙar mai shafuka bakwai, wadda aka rubuta a ranar 12 ga Oktoba, 2026, ta nuna cewa INEC ta karɓe ta a ranar 13 ga Oktoba.

Ta hannun lauyoyinsa, Garry ya buƙaci hukumar ta binciki kundin rajistar mambobin PDP, domin tabbatar da ko jam’iyyar ta cika sharudan doka kan gabatar da bayanan mambobinta da tsayar da ’yan takara.

Lauyoyin sun ce ya kamata INEC ta tabbatar da ko an shigar da sunan Pantami cikin kundin rajistar mambobin jam’iyyar kafin wa’adin da doka ta kayyade ya ƙare.

Bayani kan dokar zaɓe ta 2026

Ƙungiyar lauyoyin ta kafa hujjojinta kan sashe na 77 na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya tanadi gabatar da kundin rajistar mambobin jam’iyyun siyasa ga INEC cikin lokacin da doka ta tsara.

Sun kuma ambaci hukuncin Kotun Ƙoli a shari’ar INEC da Zenith LP, mai lamba SC/CV/495/2026, wanda aka yanke a ranar 24 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi sabon bidiyo ya kira Tinubu da 'Bola' duk da APC ta yi gargadi

A cewar lauyoyin, zargin cewa Pantami ya shiga PDP ne bayan wa’adin gabatar da kundin rajistar mambobin jam’iyyar ya ƙare, ya haifar da tambayoyi kan cancantarsa ta shiga zaɓen fitar da gwani na gwamnan jihar.

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe. Hoto: Legit
Source: Original

Legit ta tattauna da Aminu

Wani da ke tafiyar Pantamiyya a jihar Gombe, Aminu Abdullahi ya bayyana wa Legit Hausa cewa har yanzu ba su karaya ba.

Aminu ya ce:

"Muna fatan samun nasara duk da abubuwan da suke faruwa da mu. Ba mu karaya ba, kuma muna nan sai mun ga abin da ya turewa buzu nadi."

Ya kara da cewa za su cigaba da addu'a domin ganin gwaninsu ya samu mafita duk da kalubalen da ya ke fuskanta.

Kwankwaso ya yi kira ga Atiku

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa yake son Atiku Abubakar, ya janye wa Peter Obi, a zaɓ

2027.

Kwankwaso, wanda ya ce yana da dadaddiyar alaƙar siyasa da Atiku, ya amsa da cewa yana son tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ajiye burinsa na neman shugabancin ƙasa a wannan karon.

Ya bayyana cewa ya yi amfani da ziyarar wata tawagar Fulani daga sassa daban-daban na ƙasar zuwa gidansa wajen roƙonsu su tattauna da Atiku kan janyewar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng