Ana Shirin Zaben 2027, Tinubu Ya Nada Sababbin Kwamishinoni 6 INEC
- Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sababbin kwamishinonin shida a hukumar zabe mai zaman kanta, INEC yayin da ke tunkarar zaben 2027
- Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai Farfesa Mustapha Aliu da Bashir Muhammed Umar, waɗanda za su wakilci Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya
- Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance waɗanda aka naɗa gabanin babban zaɓen da za a gudanar a watan Janairu mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin kwamishinonin zabe shida domin cike guraben da suka samu a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Daga cikin wadanda Tinubu ya nada akwai kwamishinonin INEC na kasa guda hudu da kuma kwamishinonin zabe na jihohi guda biyu.

Source: Facebook
Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman kan yaɗa labarai da dabaru, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a X ranar Juma’a.
Onanuga ya ce naɗin waɗanda aka zaɓa yana jiran amincewar Majalisar Dattawa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeirya ya tanada.
An sake naɗa Dr Bala Bila a matsayin kwamishinan INEC na ƙasa mai wakiltar yankin Arewa maso Gabas.
Sunayen sababbin kwamishinonin ƙasa
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana sunayen sabbin kwamishinonin ƙasa kamar haka:
- Farfesa Mustapha Aliu: Zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru a matsayin wakilin yankin Arewa maso Yamma
- Bashir Muhammed Umar: Zai maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu a matsayin wakilin yankin Arewa ta Tsakiya
- Mrs Oluwatoyin Babalola: Shugaba Tinubu ya gabatar da sunanta a matsayin sabuwar kwamishinar ƙasa mai wakiltar Kudu maso Yamma. A halin yanzu, ita ce kwamishinar zaɓe ta jihar Osun
Oluwatoyin Babalola za ta maye gurbin Farfesa Cornelius Ajayi, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 24 ga Oktoba.
Sabbin kwamishinonin zaɓe na jihohi
Shugaba Tinubu ya kuma zaɓi sababbin kwamishinonin zaɓe na jihohi biyu.

Kara karanta wannan
"Sun tsorata," Kwankwaso ya gano sasu shirin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Wadanda ya zaba u ne Dr Samuel Akinjide Akinleye, tsohon babban sakatare mai ritaya, wanda zai wakilci jihar Ekiti, da Zahradden Basiru Sanusi daga jihar Jigawa, wanda zai maye gurbin Farfesa Saidu Ahmed Babura.

Source: Facebook
Shugaban ƙasar ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance waɗanda aka naɗa tare da amincewa da su, la’akari da babban zaɓen da ke tafe a watan Janairu mai zuwa.
Tinubu ya ba ɗan tsohon gwamna mukami
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Yakubu Jang, ɗan tsohon gwamnan Filato, Jonah Jang , a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ƙasa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya sanar da naɗin yayin bikin cika shekaru 80 da ƙaddamar da littafin tarihin Jonah Jang a Jos, babban birnin jihar Filato.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan , gwamnoni, jami'an gwamnatin tarayya da na jihohi, sarakunan gargajiya da sauran fitattun mutane a sassan kasar nan.
Asali: Legit.ng
