Kyakkyawar Budurwa Da ke Zama a Legas Ta Baje Kolin Gidanta da Take Biyan Haya N800k Duk Shekara

Kyakkyawar Budurwa Da ke Zama a Legas Ta Baje Kolin Gidanta da Take Biyan Haya N800k Duk Shekara

  • Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa tana samun wutar lantarki awa 24 a kullun
  • Da take nuna tsarin dakinta, matashiyar ta ce bata so yanayin yadda aka gina bandakinta ba
  • Bayan zagayen dakin nata, ta soya kwai sannan ta bayar da shi ga matashin da ke duba gidan nata

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta bayyana wa wani matashi mai suna @walesmorqan yawan kudin da take biya na hayar gidanta duk shekara a jahar Legas.

Matashiyar na daya daga cikin mutanen da suka amsa tambayoyi kan abun da suke biya na hayar gidansu a bidiyo. Bayan ta bayyana cewa tana biyan N800,000 duk shekara, sai ta zagaya da shi cikin bangaren nata.

Budurwa da daki
Kyakkyawar Budurwa Da ke Zama a Legas Ta Baje Kolin Gidanta da Take Biyan Haya N800k Duk Shekara Hoto: @walesmorqan
Asali: UGC

Mazauniyar Legas na biyan kudin haya N800k duk shekara

Kara karanta wannan

Assha: Ba a gama da jimamin Hanifa ba, wasu matasa sun sace yarinya mai shekaru 6 a Kano

Yan sakonni da fara bidiyon, ta nunawa matashin kwaban kayanta da shukokinta, wanda suna daga cikin abun da take alfahari da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Budurwar ta kuma bayyana cewa gidan na zuwa da wutar lantarki na awa 24. A karshen bidiyon, ta baiwa mutumin abinci ya ci.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama’a

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

kolabbola ya ce:

“Tana da kirki amma susu bata jin magana, barka da zuwa rayuwar yarinya mara ko sisi da ke zama a Legas, idan ka sani ka sani.”

nero ya ce:

“Yarinyar nan na da fadar gaskiya dan Allah.”

rusy104 ta ce:

“Babu wanda ya kula da kwamfutar MacBooks guda biyu??????”

king coco ya ce:

“Tana da kula. Ta tambayi ko yana jin yunwa ba kowa ne ya fahimci cewa mutum zai so cin abinci ba.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Matshi Da Yaje Ba Haya A Dawa Karke Da Fada Da Damisa Wadda Ta Jikkatashi

Sinzah ya ce:

“Dan Allah a wani bangare take zama saboda 800k kan wannan gaba daya ya yi.”

CHINECHEREM ya ce:

“Za ka ci abinci, yallabai ya ce a’a. Baaaba na yi ihu da na gansa yana cin abinci.”

Budurwa ta yi fentin dakinta da kanta

A wani labari, wata budurwa ta ba da mamaki soshiyal midiya bayan ta wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda ta yi fentin dakinta da kanta.

Budurwar ta je kasuwa ta sayo fentinta guda biyu sannan ta kama aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel