'Yan Sandan Jihar Kwara Sun Ceto Yara 41, Sun Kama Wasu da Ake Zargi da Laifin Safarar Mutane

'Yan Sandan Jihar Kwara Sun Ceto Yara 41, Sun Kama Wasu da Ake Zargi da Laifin Safarar Mutane

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara sun kama wasu mutum hudu da ake zargin sun sato yara daga Arewa za su kai Kudu
  • An kama su tare da yara 41 suke shirin kaiwa wani faston da ba a bayyana sunansa ba ya zuwa yanzu
  • Ana ci gaba da bincike, kuma za a tabbatar da gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifukan a kotu

Ilorin, jihar Kwara - Rundunar 'yan sandan jihar Kwara ta ce ta kama wasu mutum uku da ake zargi da aikata safarar mutane daga jihar Neja zuwa birnin Ilorin.

Wannan na fitowa ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Osakanmi Ajayi ya fitar a Ilorin a ranar Asabar, inda ya bayyana yadda lamarin ya faru, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: NNPC ta Bayyana Lokacin Fara Hako Mai a Sabuwar Jiha a Arewacin Najeriya

A cewar sanarwar, wadanda aka kaman sun hada da Musa Ayuba, Jeremiah Muda da Luka Ayuba, kuma duk taso ne daga karamar hukumar Kwantagora ta jihar Neja.

An kama wasu da ke shirin kaiwa fasto yaran da suka sato daga Arewa
'Yan Sandan Jihar Kwara Sun Ceto Yara 41, Sun Kama Wasu da Ake Zargi da Laifin Safarar Mutane | Hoto: headtopics.com
Asali: UGC

An kama masu safarar mutane da yawa 41

A cewar kakakin, an kame wadanda ake zargin ne a kusa babban titin Okolowo a ranar Asabar tare da yara 41 da suke jiran a kai su wani wuri da ba a sani ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani bangaren sanarwar ya ce:

"Yaran da aka saton suna shekaru mabambanta daga biyar zuwa 15."

Yadda suka tsara aikata laifin

Ya kuma bayyana cewa, yayin da aka yi bincike, an gano wadanda ake zargin sun tsara haduwa ne a birnin Ilorin bayan tasowa daga jihar Neja domin mika su ga wani fasto, Premium Times ta ruwaito.

Sanarwar ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

Assha: Ba a gama da jimamin Hanifa ba, wasu matasa sun sace yarinya mai shekaru 6 a Kano

"A yanzu haka yaran suna tare da rundunarmu, kuma nan kusa za mu tuntubi iyayensu da sauran hukumomin da suka dace.
"Kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara, Paul Odama na ba da shawari ga iyaye da masu rike da yara da su guji sakin 'ya'yansu ga wadanda basu sani ba.
"Watakila za a yi amfani da yaran ne a matsayin 'yan aiki da kuma wasu ayyukan wahalan, wadanda sun saba dokar hakkin yara.
"Za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan kammala bincike yadda ya dace."

Yadda mai reno ta ci amana, ta shafawa jariri HIV

A wani labarin kuma, wata mata ta yi barna ta hanyar shafawa jariri HIV a lokacin da aka ba ta damar yin aikin reno.

An ruwaito cewa, matar ta ba yaron cutar ne ta hanyar shayar da shi nononta ba tare da izinin iyayensa ba.

Jama'a a kafar sada zumunta sun ba da shawarin a kama matar tare da daure ta, domin da gangan ta yi.

Kara karanta wannan

Ribas: ‘Yan Sanda Sun Damke Yaro Mai Shekaru 17 da Yayi wa Mata 10 Ciki

Asali: Legit.ng

Online view pixel