'Yan Sanda Sun Kama Wasu Matasa 3 da Laifin Sace Yarinya ’Yar Shekara 6 a Kano

'Yan Sanda Sun Kama Wasu Matasa 3 da Laifin Sace Yarinya ’Yar Shekara 6 a Kano

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kame wasu matasa da ake zargin sun sace wata yarinya 'yar shekara shida a Kano
  • Wannan na zuwa ne watanni bayan da aka gano wani malamin makaranta ya sace dalibarsa ya nemi kudin fansa duk dai a Kano
  • Ana yawan samun aukuwar sace-sacen mutane a Arewacin Najeriya, lamarin na kara tada hankalin jama'ar yankin

Jihar Katsina - Rahoton da muke samu daga Katsina ya bayyana cewa, sanda sun kwamushe wasu matasa uku bisa zargin yin garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara shida.

Rundunar ta bayyana sunayen matasan da ake zargin da Aliyu Salisu, Abdulrazak Ibrahim, da kuma Mohammed Ibrahim, kuma an ce dukkansu ‘yan shekara 19 ne kacal.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ya fitar da wata sanarwa a ranar Laraba, inda yace matasan sun hada baki ne tare da yin awon gaba da yarinyar a unguwar Bachirawa da ke jihar Kano a ranar 6 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Damke Wasu Matasa Uku Kan Yin Garkuwa Da Yarinya Yar Shekara 6 a Wata Jahar Arewa

Matasa sun sace yarinya mai shekaru 6 a Kano
'Yan Sanda Sun Kama Wasu Matasa 3 da Laifin Sace Yarinya ’Yar Shekara 6 a Kano | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Isah ya kuma bayyana cewa matasan sun nemi a ba su kudin fansa Naira miliyan biyu, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama matashi a lokacin da yake shirin karbar kudin fansa

Gambo Isah ya shaida cewa, an kama daya daga cikin tsagerun matasan ne a lokacin da yake yunkurin karbar kudin fansan Nnaira miliyan biyu, rahoton jaridar Punch.

A cewar sanarwar:

“Sun sace Fatima Abubakar, ‘mace’, ‘yar shekara 6, da ke zaune unguwar Bachirawa a jihar Kano a ranar 06/01/2023 da misalin karfe 11:00 na safe suka tafi da ita jihar Katsina tare da neman kudin fansa har Naira miliyan biyu (N2,000,000.00).
“An kama wanda ake zargin (Aliyu Salisu da ake kira “Chilo”) a wajen karbar kudin fansa.
"Bayan yin bincike, an kama sauran abokan harkallarsa kuma an ceto wacce aka sace ba tare da wani rauni ba."

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Yan Bindiga Suka Halaka Amarya da Ango Yan Kwanaki Kafin Aurensu

Jaruman ’Yan Banga Sun Kwamushe Wasu ’Yan Ta’adda 5 a Jihar Bauchi

A wani labarin kuma, kunji yadda wasu jaruman 'yan banga suka kai ga nasarar kwamushe wasu 'yan ta'adda a jihar Bauchi.

An kuma bayyana cewa, an ceto wasu mutum biyar da 'yan ta'addan suka sace a wasu yankunan jihar ta Arewa maso Gabas.

Jami'ai a Najeriya na samun nasara kan tsagerun 'yan ta'addan da ke addabar mutane a yankunan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel