Lakcaran Najeriya da Matarsa Ta Haifi Jarirai 5 Ya Magantu, Ya Ce Ya Manta Yaushe Rabonsa da Albashi

Lakcaran Najeriya da Matarsa Ta Haifi Jarirai 5 Ya Magantu, Ya Ce Ya Manta Yaushe Rabonsa da Albashi

  • Allah ya albarkaci matar wata mata lakcara a Najeriya ta hanyar azurta ta da haihuwar jarirai biyar nan take
  • An ce mai jegon ta kasance malama a jami'ar Nnamdi Azikwe da ke binrin Awka a jihar Anambra
  • Jama'ar kafar sada zumunta sun taya su murnar samun jarirai mata har biyar, sun kuma nemi hanyar taimakonta

Wata mata, Mrs Ngozi Uzodike ta girgiza intanet yayin da ta shiga murna bayan haihuwar yara biyar nan take.

A wani rahoton Punch, an ce matar tana aikin karantarwa ne a jami'ar Nnamdi Azikwe, a tsangayar ilimin harkar kasuwanci.

Mata ta haifi jarirai 5, ana binta bashin N19m a asibiti
Lakcaran Najeriya da Matarsa Ta Haifi Jarirai 5 Ya Magantu, Ya Ce Ya Manta Yaushe Rabonsa da Albashi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daya daga jariran ya mutu

A cewar rahotanni, Ngozi ta haifi jariranta biyar ne a asibitin yara da mata na Obijackson da ke Okija a jihar Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Anambra: Malamar Jami'a ta Haifa Yara 7 Reras, Tana Neman Daukin Jama'ar Annabi

Sai dai, abin takaici ya rasa daya daga cikin jariran nan take lokacin da aka haife shi.

Tana bukatar taimako

Rahotannin da ke fitowa daga yankin sun ce, ana neman N19m na kudin jinya da aka yi mata a asibitin.

Sai dai, matar ta ce rabonta da ganin albashi har ta manta; ta fara aiki a jami'ar a shekarar 2020 ta Korona.

Ta bayyana neman taimako daga ilahirin jama'ar duniya da za su iya tallafa mata wajen warware wannan tarun kudi na jinyta.

Da yawan jama'a suna ta taya ta murna a kafar sada zujunta, wasu sun bayyana neman ta yadda za su taimaka mata.

Martanin jama'ar intanet

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:

@TobestOkafor:

“Kaii amma dai ya yi yawa Allah na ba da kyautar 'ya'ya. Kenan ya kamata ki biya duk da naki ne."

@auwalumuhammadfagge:

“Allah mai bayarwa ne a lokacin da baka yi tsammani ba."

Kara karanta wannan

Ribas: ‘Yan Sanda Sun Damke Yaro Mai Shekaru 17 da Yayi wa Mata 10 Ciki

@therespakels:

“A haka kike tunanin 1 ne yasa kika haifi yaran. Yi amfani da kanki."

@AndalineChidera:

“Ina ma ace zan iya taimaka mata a wannan lokacin...bai baci ba, ku tura min lambarta."

@udubonch_c:

“Allah ya raya ya kuma kare su gaba daya. Kasancewar sun kawo miki farin ciki a rayuwa, ALlah yasa hakan ya tabbata, Ameen."

@priieest19:

“Neman taimako? Wannan ya yi sosai. Allah ya taimake ta ta iya kula yaran."

@HumpheryOnyeama:

“Kudi 19m... Ahhh meye haka ne kam... kamar hakan da hauka a ciki...Jesu."

Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan haihuwa ba, wata dalibar jami'a a Najeriya ta taba haihuwar jarirai 5 nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel