Ana Batun Cire Sunayen Wasu Yan Takara, Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Yi Murabus
- Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Cross River, Venatius Ikem ya yi murabus daga daga mukaminsa sakamakon rikicin da ya barke a jam'iyya
- Mista Ikem a bayyana cewa rikicin cikin gida na raunana ƙarfin jam’iyyar PDP yayin da lokacin zaɓe ke gabatowa
- Ya gode wa Sanata Sandy Onor, Sanata Jarigbe Agom Jarigbe da sauran magoya bayansa bisa goyon bayan da suka ba shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Cross River, Nigeria - Jam’iyyar PDP a jihar Cross River ta shiga rikicin shugabanci bayan shugaban jam’iyyar na jihar, Venatius Ikem, Esq., ya yi murabus.
Ikem ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne saboda rashin alkibla da rigingimun cikin gida da suka addabi PDP a jihar.

Source: Facebook
Venatius Ikem ya sanar da murabus ɗinsa ne a cikin wata wasiƙa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 16 ga watan Oktoba, 2026.
Ya aika wasiƙar ga Sakataren PDP na kasa a hedikwatar jam'iyya da ke Wadata Plaza a Abuja, da kuma Sakataren jam’iyyar na jihar Cross River.
Dalilin murabus din shugaban PDP
A cikin wasiƙar, ya ce:
“Cikin baƙin ciki da kuma cikakken sanin nauyin da ke kaina, tare da jajircewa ga ƙa’idojin da nake darajawa, ina sanar da murabus ɗina daga matsayin shugaban jam’iyyar PDP na reshen jihar Cross River, wanda zai fara aiki nan take.”
Ya bayyana cewa shawarar ta kasance mai matuƙar wahala, amma ya zama dole ya ɗauke ta bayan yin nazari mai zurfi kan halin da jam’iyyar ke ciki a yanzu.
A cewarsa, ba zai iya ci gaba da gudanar da aikinsa yadda ya kamata a matsayin shugaban jam’iyyar ba a yanayin da take ƙara karya ƙa’idoji, haɗin kai da manufar bai ɗaya da ya kamata su jagoranci ayyukan PDP
Ikem ya ce yayin da jam’iyyar PDP ke shirin shiga wani muhimmin lokacin zaɓe, yana ƙara samun wahalar daidaita nauyin da ke kansa na shugabancinda yadda abubuwa ke gudana a cikin gida.
PDP na fama da rikicin cikin gida
Ya ce:
“A ra’ayina bayan yin nazari mai zurfi, jam’iyyar PDP a halin yanzu na fama da rikici, da rashin haɗin kai a shugabanci.
“Waɗannan ƙalubale sun rage tasirin ayyukanmu sosai, kuma idan ba a magance su ba, za su iya kawo cikas ga sadaukarwa, jarin da aka zuba da kuma burin mambobi da suka yi aiki tuƙuru domin ganin jam’iyyar ta yi nasara.”

Source: Twitter
Duk da rikicin da jam’iyyar ke fuskanta, Ikem ya nuna godiyarsa bisa damar da aka ba shi na yi wa PDP hidima tsawon shekaru biyar da suka gabata.
Ya gode wa Sanata (Farfesa) Sandy Onor da Sanata Jarigbe Agom Jarigbe bisa ƙarfafa masa gwiwa da goyon bayan da suka ba shi.
Dan takarar PDP ya sauya sheka
Kun ji cewa ɗan takarar PDP na mazabar Ibadan ta Arewa maso Gabas a zaɓen 2027, Hammed Taoreed Ademola, da ɗan takarar Accord, Adedapo Ojo, sun koma jam'iyyar APC.
Ademola, wanda aka fi sani da Lucky, ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin PDP ne bayan ya gudanar da bincike kan yanayin siyasar ƙasar
Asali: Legit.ng

