Magidanci: Yadda na Fatattaki Mahaifiyata Daga Gidana Bayan Ta Mari Matata

Magidanci: Yadda na Fatattaki Mahaifiyata Daga Gidana Bayan Ta Mari Matata

  • Wani sabon ango 'dan Najeriya ya fatattaki mahaifiyarsa da ta tsugunna ta haife shi daga gidansa kwanaki biyu bayan ta kai masa ziyara da yayi sabon aure
  • Mutumin mai karancin shekaru ya bayyana yadda ya dawo gida ya gano yadda mahaifiyarsa ta gaurawa sabuwar amaryarsa mari
  • Bayan iya kokarin da yayi don nunawa mahaifiyarsa kuskurenta bai yuwu ba, ya yanke shawarar korarta daga gidansa kada ta kashe masa aure

Wanu mutumi 'dan Najeriya cikin kwanakin nan ya labarta kalubalen da ya fuskanta daga mahaifiyarsa, wacce ta kai mai ziyara gidan aurensa a karo na farko.

Mutumin ya auri masoyiyarsa, inda mahaifiyarsa ta yanke shawarar kai musu ziyara a karo na farko.

Magidanci mai korar mahaifiya
Magidanci: Yadda na Fatattaki Mahaifiyata Daga Gidana Bayan Ta Mari Matata. Hoto daga @Jodi Jacobson, Ivan Pantic/Getty images
Asali: Getty Images

Sai dai, bayan isarta gidan, ta fara neman rikici da matar tasa har ta kai ga ta daga hannu ta tsinke ta da mari.

Kara karanta wannan

Matar Aure Mai Ciki Ta Kama Mijinta Na Sharholiya da Abokiyar Aiki, Bidiyon Ya Girgiza Jama'a

Yayin da yayi bincike ya nemi ganar da ita kuskurenta, matar ta murje ido ta ki amincewa da hakan, sai ma ta cigaba da neman wani rikicin a gidan auren 'danta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan ya fusata 'dan, wanda ya kasa danne fushinsa, inda ya koreta daga gidan.

Dexterouz11, wanda ya wallafa labarin a dandalin Twitter ya ce:

"Mutumina ya ce mahaifiyarsa ta kaiwa amaryarsa ziyara karo na farko gidan aurensu amma ya koreta bayan kwanaki biyu.
"Ta yi rikici da matarsa gami da dauke yarinyar da mari. Mutumin ya dawo ya ji ba'asin lamarin, inda ya gano laifin mahaifiyarsa ne.
"Ta ki yarda saboda ita uwa ce. Ta cigaba da neman rikici a gidan har ta kai ga ya koreta daga gidan a rana ta biyu. Sabbin ma'aurata ku guji barin danginku na kai muku ziyara gidan aurenku."

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: DPO ya Yanke Jiki Ya Fadi a Ofishinsa, Ta Rasu a Take

Ga wallafar a Twitter:

Yayin da Legit.ng ta tuntubi Dexterouz11 don jin karin bayani game da lamarin, ya bayyana yadda mahaifiyar mutumin ta daina masa magana daga lokacin.

"Shi da mahaifiyarsa ba su kara magana da juna ba bayan ya koreta daga gidan. Mahaifiyarsa ta ce ba za ta taba yafe hakan ba. Amma yanzu matarsa na cikin kwanciyar hankali, daman hakan yafi mahimmanci."

Malamar Jami'a ta haifa yara 7, tana neman taimakon jama'a

A wani labari na daban, wata malamar jami'ar UNIZIK ta santalo yara har bakwai a haihuwa daya.

Yaran biyar mata sai biyu maza duk sai sun samu kulawar likita sannan za su samu lafiya, hakan zai ci makuden miliyoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel