Tashin Hankali Yayin da Mai Reno Ta Shayar da Jariri, Ta Shafa Masa HIV Ba a Sani Ba

Tashin Hankali Yayin da Mai Reno Ta Shayar da Jariri, Ta Shafa Masa HIV Ba a Sani Ba

  • Ana zargin wata mata mai reno da shayar da jaririn da aka ba ta reno tare da shafa masa cutar HIV/AIDS
  • Iyayen jaririn sun dauke shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa bayan da ya kwanta rashin lafiyar da ya gaza warkewa
  • Cikin lamari mai ban mamaki aka gani yana dauke da cutar HIV, kuma ana kyautata zaton mai renonsa ne ta shayar dashi cutar a nono

Wata mata mai renon jaririn uwar dakinta ta ba jaririn nononta, yaro ya kamu da cutar HIV mai karya garkuwar jiki.

@talkradio702 ne yada wannan mummunan labarin a kafar TikTok, tare da bayyana yadda lamarin mara dadi ya faru.

A cewar labarin da aka yada, mai renon ta kasance tana shayar da yaron a lokacin da iyayensa ba sa gida kuma ba tare da izininsu ba.

Kara karanta wannan

Rike Fitsari Ko Kinyinsa Da Wuri Na Janyo Matsalar Koda A Jikin Dan Adam

Mai reno ta shafawa jariri HIV
Tashin Hankali Yayin da Mai Reno Ta Shayar da Jariri, Ta Saka Masa HIV Ba a Sani Ba | Hoto: DMEPhotography and Resolution Productions/ Getty Immages. (Photos for illustration).
Asali: UGC

Labarin mai renon da ta shafawa yaro HIV/AIDS

A lokacin da aka ga yaron ya yawaita rashin lafiya kuma ya gaza samun sauki, an kaishi asibiti domin binciken lafiyarsa. Daga nan ne aka gano yaron yana dauke da cutar sida mai karya garkuwar jiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyayen yaron sun shiga tashin hankali kasancewar sun haifi yaron ba tare da wata cuta ba hakazalika su ma lafiyarsu lau.

Bincike ya tabbatar da cewa, mai renon ce ke dauke da cutar kuma ta shafa ma yaron ne ta hanyar shayar dashi mama.

Jama'a a kafar sada zumunta sun shiga mamaki, sun kuma bayyana martani mai daukar hankali.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'ar TikTok

@dikelediDR1990:

"Tun farko meye tasa mai reno za ta shayar da yawo."

@user7799101400479:

"Ya kamata a kama mai renon domin ta san abin da take yi."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

@simnikiwebangelo:

"Haka ya faru dani da na daya tilo yana da cutar ni kuma bani dashi, kakarsa ce ta shafa masa. Ba zan taba mantawa ba."

@narematlakala58:

"Na taba kama mai renon yaro na tana ba shi mama a 2010 amma aka yi sa'a bai kamu ba duk da cewa cutar tata ta yi tsanani. Muna rayuwa a duniya mai cike da cuta."

@Tinyiko ta Pelembe:

"Allah ya kare yaranmu daga abubuwan da ba za mu iya ba."

@Bruce Spiroza:

"Wannan babban lamari ne ya kamata a kame mai renon"

Likitoci 199 Cikin 280 a Jihar Zamfara Ma’aikatan Bogi Ne, Inji Gwamna Matawalle

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Zamfara ya bayyana kadan daga abin da ke faruwa a ma'aikatar lafiya a jiharsa.

A cewarsa, akalla likitoci 199 ne da ke karbar albashi alhali babu su kwata-kwata da sunan ma'aikata a jihar.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Magana Game Da Jarumar Da Take Fitowa A Shirin Nan Mai Dogon Zango Na Amaryar Tik-Tok

Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan ba a aikin gwamnati a Najeriya, an sha samu a wasu lokutan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel