Abuja
Lauya mai rajin kare hakkin bil’adama, Deji Adeyanju, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kama Sheikh Ahmad Gumi kan kalaman da ya yi kan matsalar tsaro.
Wani matashi da ke yin bautar kasa ya shiga hannun ‘yan sanda bayan zarginsa da kashe mahaifinsa, fitaccen ɗan kasuwa Adimike Godwin, bayan gardama kan kuɗi a Abuja.
Janar Theophilus Danjuma ya bayar da N3bn yayin kaddamar da littafin tarihin Yakubu Gowon a Abuja, yayin da Aliko Dangote ya sayi kwamitin littatafan a kan N500m.
Kashim Shettima ya bayyana yadda wasu mutane suka fadawa Bola Tinubu cewa yana shirin kashe shi domin karbar mulki bayan sun hau gwamnati a shekarar 2023.
Jam’iyyar LP mai adawa karkashin jagorancin Julius Abure ta sanar da cewa za ta shiga zaben 2027 tare da bayar da fom kyauta ga masu takara a dukkan matakai.
DSS ta gurfanar da Nasir El-Rufai a kotun tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi tsaron kasa, inda ya musanta zarge-zargen.
Babbar Kotun Tarayya ta bai wa Nasir El-Rufai beli kan N100m tare da sharuddan zuwa DSS duk wata da gabatar da mai tsaya masa mai gida a Abuja da wasu sharudda.
Iyalan Malam Nasir El-Rufa'i sun ce hukumar ICPC ta hana mahaifinsu ganin likita duk da bukatar hakan tare da hana matatar shi mika masa abincin dare.
Najeriya da Jamus sun ƙulla sabuwar yarjejeniyar haɗin gwiwa kan noma, makamashi, fasaha da bunkasa tattalin arziki tare da tallafin euro miliyan 65.
Abuja
Samu kari