Babu Imani: Wani Ɗan Masu Kuɗi Ya Caccaka wa Mahaifinsa Wuka har Lahira a Abuja

Babu Imani: Wani Ɗan Masu Kuɗi Ya Caccaka wa Mahaifinsa Wuka har Lahira a Abuja

  • Wani matashi ɗan bautar ƙasa ya shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin kashe mahaifinsa, fitaccen ɗan kasuwa Adimike Godwin, a Abuja
  • An ce lamarin ya faru ne yayin da takaddama ta barke tsakanin mamacin da dansa kan yadda ake tafiyar da kasuwanci da batun barnatar da kudi
  • Rundunar ‘yan sandan Abuja ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cafke mutane biyar domin gudanar da bincike kan mutuwar marigayin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wani ɗan bautar ƙasa (NYSC), ya shiga hannun ‘yan sanda bayan zarginsa da kashe mahaifinsa, Mista Adimike Godwin, a yankin Guzape da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin, wanda fitaccen ɗan kasuwa ne a harkar kayan lantarki da gidaje, ya mutu ne bayan an caccaka masa wuƙa a jikinsa.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga zargin yana yi wa Tinubu aiki a NDC

Ana zargin wani yaro ya kashe mahaifinsa a Abuja.
Kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh. Hoto: @jossyadeh
Source: Twitter

Yadda rikicin uba da ɗa ya barke

Wata majiya daga ƙungiyar masu sayar da kayan lantarki ta Najeriya (EDAN) ta shaida wa jaridar Vanguard cewa Godwin ya kasance babban ɗan kasuwa mai gidaje a Legas da Abuja.

Majiyar ta ce marigayin ya je Abuja ne domin ganin babban ɗansa wanda ke yi wa ƙasa hidima kuma yake kula da wasu kadarorinsa.

A cewar majiyar, matashin ya dawo gida daga wajen shakatawa kafin rikici ya barke tsakaninsa da mahaifinsa.

Majiyar ta ce:

“Mun samu labarin cewa ɗaya daga cikin manyan ‘yan kasuwar mu ya mutu a wani mummunan yanai. Mutumin yana da babban shigo kuma yana harkar gidaje.
“An ce ɗansa, wanda ake zargin yana amfani da miyagun ƙwayoyi, ya dawo daga gidan rawa sannan suka fara gardama kan kuɗi da yadda mahaifinsa yake kula da shi idan aka kwatanta da ‘ya’yan wasu attajirai."

Ana zargin ya caka masa wuƙa

Kara karanta wannan

Ana zargin Tinubu ya sake samun matsala da Shettima, zai iya shafar kujeransa

Majiyar ta ƙara da cewa gardamar ta ƙara tsananta ne bayan mahaifin ya kawo batun yadda yaron yake tafiyar da kuɗaɗen kasuwanci.

Ta kara da cewa:

“Bayan wannan taƙaddama, an ce ya caka wa mahaifinsa wuƙa har sau uku a sassa daban-daban na jikinsa. Yanzu haka yana hannun ‘yan sanda a Abuja.”

Majiyar ta kuma bayyana cewa matar mamacin na daga cikin waɗanda aka gayyata domin amsa tambayoyi yayin da bincike ke ci gaba.

Ƙungiyar EDAN ta ce ta ɗauki matakin kulle shaguna da ma’ajin kaya na marigayin domin hana satar kayayyaki, kamar yada jaridar The Nation ta ruwaito.

“Wannan shi ne tsarin da muke bi idan wani daga cikin mambobinmu ya shiga irin wannan ibtila’i,” a cewar majiyar.
an cafke wani yaro da ake zargin ya kashe mahaifinsa a Abuja.
Alamar shiga babban birnin tarayya Abuja. Hoto: Peeterv via Getty Images
Source: Getty Images

‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

Da aka tuntubi jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce an gano mamacin ne bayan an kai rahoton gaggawa saboda an kasa samun damar tuntubarsa.

“A lokacin da jami’anmu suka isa wurin, sun tarar da mutumin cikin jini. Daga bisani likitoci a babban asibitin Karu suka tabbatar da mutuwarsa,” in ji SP Adeh.

Kara karanta wannan

Hayatudeen: "Matakin da zan dauka kan 'yan bindiga idan na zama shugaban kasa"

Ta ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sanda na Abuja, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

SP Adeh ta ce mutane biyar ciki har da wani ɗan uwa na mamacin suna tsare domin bincike.

Matashi ya kashe mahaifinsa a Jigawa

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa, 'yan sanda sun tabbatar da cafke wani matashi da ake zargi da sassara mahaifinsa da adda har ya mutu a Jigawa.

Lamarin ya faru ne a unguwar Bakin Kasuwa da ke yankin Sara, inda ake zargin matashin mai shekaru 20 ya kai wa mahaifinsa harin da ya jawo rasuwarsa.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar ya umarci a mayar da binciken lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar (SCID) da ke babban birni Dutse.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com