An Nemi a Kama Sheikh Ahmad Gumi Game da Kalamansa kan Ta’addanci a Najeriya
- Lauya mai rajin kare hakkin bil’adama ya bukaci gwamnatin tarayya ta kama Sheikh Ahmad Abubakar Gumi kan kalaman da ya yi kan matsalar tsaro
- Mai fafautukar kare hakkin bil Adama ya ce duk wanda ke nuna goyon baya ko tausaya wa ‘yan ta’adda ya kamata a dauke shi tamkar dan ta’adda
- Sheikh Gumi ya bayyana a wani bidiyo cewa Fulani makiyaya wani bangare ne na al’umma, yana mai cewa dole Najeriya ta koyi zama tare da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Lauya mai rajin kare hakkin bil’adama, Deji Adeyanju, ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta kama fitaccen malamin addinin Musulunci.
Adeyanju yana magana kan malamin mai suna Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi bayan kalamansa game da yan ta'adda.

Source: Facebook
Adeyanju ya yi wannan kira ne a rubutun da ya yi a shafinsa na Facebook a yau Laraba 20 ga watan Mayun shekarar 2026.
Maganar da ta jawo wa Ahmad Gumi suka
Hakan ya biyo bayan wani bayanin Gumi wanda Vanguard ta samu inda aka zargi Sheikh Gumi da kare ‘yan bindiga.
A cikin bayanin, malamin ya ce Fulani makiyaya wani bangare ne na al’umma, yana mai cewa dole mutane su koyi zama tare da su.
Da yake mayar da martani, Adeyanju ya ce duk wanda ke tausaya wa ‘yan ta’adda tamkar dan ta’adda ne.
Ya ce kasar da ta gaza ce kawai za ta bari mutane masu irin wadannan kalamai su ci gaba da rayuwa ba tare hukunci ba.

Source: Twitter
Bukatar lauyan ga jami'an tsaro
Adeyanju ya kara da cewa kalamai da ayyukan Sheikh Gumi na iya kara ingiza ta’addanci da rashin tsaro a Najeriya gaba daya.
Ya bukaci hukumomin tsaro su kama malamin domin hakan ya zama izina ga sauran mutane masu irin wadannan ra’ayoyi a kasar nan.
Rahoton ya nuna cewa wannan batu ya sake jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kan matsalar tsaro da kalaman addini a Najeriya.
Lauyan ya ce abin takaici ne yadda mutane irinsu Sheikh Gumi ke rayuwa a Najeriya inda ya ce hakan kawai zai faru ne a kasar da babu gwamnati.
Ya ce irin kasar da babu gwamnati ce kawai irin su za su rayu kuma a samu wasu da ke nuna goyon baya ga yan ta'adda.
Ya ce:
“Mutane irin su Gumi za su iya rayuwa ne kawai a kasar da babu gwamnati. Masu tausaya wa ‘yan ta’adda su ma ‘yan ta’adda ne.”
Rashin tsaro: Sheikh Gumi ya dura kan Amurka
A wani labarin, an ji cewa malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya zargi hukumomin leƙen asirin Amurka da hannu a ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga a Najeriya.
Malamin ya yi zargin ne yayin martani ga Mike Arnold, fitaccen 'dan Amurka da ya sako Najeriya a gaba kan batun kashe Kiristoci da gan-dan a sassan kasar.
Martanin Sheikh Ahmad Gumi na zuwa ne a lokacin da Najeriya da Amurka ke ƙara haɗa kai wajen yaƙi da matsalar tsaro da kuma karfafa alaka a bangaren.
Asali: Legit.ng

