Sababbin Rundunonin Soji 4 za Su Fara Aikin Kakkabe 'Yan Ta'adda
- Rundunar Sojin Najeriya ta fara shirin fara aiki da sababbin rundunoni hudu da aka ƙirƙira domin faɗaɗa ƙarfin ayyukanta da yaƙi da rashin tsaro
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙara yawan rundunonin sojin daga takwas zuwa 12, tare da kafa sababbin hedikwatoci a Benue, Kwara da Taraba
- Rundunonin za su taimaka wajen rage nisan da ke tsakanin rundunar soja da wuraren da ake fuskantar barazanar ‘yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rundunar Sojin Najeriya ta fara shirin fara aiki da sababbin rundunoni hudu da aka ƙirƙira a wani mataki na sake fasalin rundunar domin ƙara ƙarfin yaƙi da rashin tsaro.
Matakin ya zo ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙara yawan rundunonin sojin Najeriya daga takwas zuwa 12.

Source: Facebook
Za a kafa sabbin hedikwatoci
Punch ta wallafa cewa sababbin hedikwatocin rundunonin za a kafa su ne a jihohin Benue, Kwara da Taraba, yayin da aka shirya kafa runduna ta 4 a jihar Edo.
Manufar sake fasalin ita ce rarraba tsarin jagoranci da kula da ayyukan soja domin ƙara saurin kai ɗauki yayin da ake fuskantar barazanar tsaro.
Matakin na kuma da nufin bai wa sojoji damar mayar da martani cikin sauri ga matsalolin tsaro da suka shafi yankuna daban-daban.
An tura bataliya zuwa Kwara
A jihar Kwara, rundunar ta ƙara dakaru sakamakon karuwar matsalolin tsaro a wasu sassan jihar, musamman satar mutane da hare-haren ‘yan bindiga.
Rundunar ta fara tura sabuwar bataliya zuwa Omu-Aran, hedikwatar ƙaramar hukumar Irepodun.
Rahotanni su nuna cewa ana kuma shirye-shiryen tura wata bataliya zuwa yankin Patigi domin ƙarfafa tsaro a yankin.
Gwamnan Kwara ya tarbi sojoji
Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce ya tarbi sojojin tare da Babban Kwamandan Sojin Najeriya, Manjo Janar Yakubu Yahaya.
Ya kuma samu rakiyar Kwamandan Sojia, Birgediya Janar Nicholas Rume, wajen karɓar sojojin.

Source: Facebook
Gwamnan ya wallafa a Facebook cewa:
“Abin farin ciki ne tarbar sojojin zuwa jihar Kwara. Ina godiya ga Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, bisa wannan gaggawar tura sojoji.”
Ya ce yana da yakinin cewa tura sojojin zai ƙara ƙarfafa ƙoƙarin samar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Sojoji sun ceto mutane Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami’an Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Ruwa, ‘Yan Sandan Najeriya, mafarauta da jami’an sa-kai sun ceto mutane 16 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
Rundunar ta ce an yi garkuwa da mutanen ne ranar Lahadi, 9 ga Agusta, 2026, lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari kan matafiya a kan hanyoyin Ojuwo–Ajengo–Memarebo da Ojiwo–Itobe.
Sojojin sun gudanar da aikin ceto tare da sauran jami’an tsaro bayan samun bayanan sirri cewa an tafi da mutanen zuwa yankin Adumu da ke ƙaramar hukumar Dekina.
Asali: Legit.ng

