Tinubu Ya Lashe Zaben Takarar Shugaban Kasa a APC da Kuri'u fiye da Miliyan 10
- Shugaba Bola Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2027 bayan samun kuri’u kusan miliyan 11 a zaben fitar da gwani
- Tinubu ya kayar da abokin takararsa daya tilo, Stanley Osifo wanda ya samu kuri’u 16,504 kacal a dukkanin mazabu 8,809 na Najeriya
- Jihohin Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma sun bai wa Tinubu gagarumar nasara yayin tattara sakamakon zaben APC a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2027 bayan samun gagarumar nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar.
Sakamakon zaben APC daga jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja ya nuna cewa Tinubu ya yi wa babban abokin hamayyarsa Stanley Osifo tazarar kuri’u mai yawa.

Kara karanta wannan
Jihohin da Tinubu ya lashe zaben fitar da gwani na APC da yawan kuri'un da ya samu

Source: Twitter
Tinubu ya samu kimanin kuri’u miliyan 11
An gudanar da zaben fitar da gwanin shugaban kasa na jam'iyyar APC ne a mazabu 8,809 a fadin Najeriya, kamar yadda rahoton BBC Hausa ya nuna.
Sakamakon da aka bayyana a cibiyar taron kasa da kasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja ya nuna cewa Tinubu ya samu kuri’u 10,999,967.
Shi kuwa Stanley Osifo ya samu kuri’u 16,504 kacal.
Gwamnonin jihohi 31 tare da manyan shugabannin APC ne suka gabatar da sakamakon jihohinsu ga kwamitin zaben fitar da gwani karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim.
Kudu ta ba Tinubu babbar nasara
A yankin Kudu maso Yamma, Tinubu ya samu gagarumar nasara musamman a jihohin da ake kallon sansanin APC.
- Legas - 814,988
- Ogun - 322,485
- Ondo - 181,996
- Oyo - 142,754
- Osun - 100,888
- Ekiti - 85,340
- Imo - 582,960.
- Enugu - 383,382
- Ebonyi - 207,579
- Abia - 161,005
- Anambra - 43,034
- Delta - 407,646
- Akwa Ibom - 389,197
- Rivers - 280,082
- Bayelsa - 227,192.
Arewa ta mara wa Tinubu baya

Source: Twitter
Jihohin Arewa maso Yamma sun nuna cikakken goyon baya ga shugaban kasa, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.
- Kaduna - 618,914
- Kano - 500,852.
- Katsina - 467,003
- Gombe - 450,517.
- Kebbi - 292,972
- Sokoto - 301,000
- Zamfara - 321,579
- Kwara - 310,990
- Nasarawa - 285,436
- Plateau - 241,720
- Kogi - 197,370
- Niger - 175,487
- Benue - 374,787
- Babban birnin tarayya Abuja - 36,103
Duk da rashin nasarar da ya samu, Stanley Osifo ya bayyana cewa zai mutunta sakamakon zaben kuma zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga jam’iyyar APC.
Kallo ya koma kan abokin takarar Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shigaba Bola Tinubu ya samu tikitin takarar APC bayan lashe zaben fitar da gwnai, yayin da hankula suka koma kan wanda zai zama mataimakinsa.
Masu sharhi sun bayyana Kashim Shettima a matsayin mataimaki mai biyayya sosai, wanda ke fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu.
Duk da rade-radin siyasa da ƙoƙarin sauya mataimaki, ana ganin cire Shettima yanzu zai iya jawo matsala ga Tinubu a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
