Matsin Lamba da Netanyahu Ke Sha daga Trump kan Isra'ilawa a Falasdinu

Matsin Lamba da Netanyahu Ke Sha daga Trump kan Isra'ilawa a Falasdinu

  • Amurka ta matsa wa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana game da ‘yan share-fage a Falasdinawa
  • Majalisar Dinkin Duniya ta ce Falasdinawa 15, ciki har da yara biyu, sun makale a gidajensu bayan an katse musu ruwa da wutar lantarki
  • Rahotanni sun ce sojojin Isra’ila sun isa wurin tare da cire tantin da ‘yan share-fagen suka kafa, yayin da ake ci gaba da takaddama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washinton DC, US - Amurka na son Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fito fili ya yi Allah-wadai da ‘yan share-fagen Isra’ila da suka killace Falasdinawa a gidajensu.

Hukumomin Amurka da Isra’ila sun bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin da ‘yan share-fagen suka kara matsin lamba kan mazauna kauyen Qusra da ke Yammacin Kogin Jordan.

Trump ya matsawa Netanyahu lamba kan mamaye Falasdinawa
Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Kusan mako guda kenan ‘yan share-fagen suna kewaye da wasu gidaje a Qusra, bayan da suka katse musu ruwa da wutar lantarki, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama fasto da ya kulla sace matan wasu malaman addini a Plateau

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ce ana ganin matakin a matsayin wani bangare na kokarin karbe karin filaye a yankin da Falasdinawa ke son kafa kasarsu.

Ambasadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, wanda ke goyon bayan matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, ya yi Allah-wadai da killace wani gidan Falasdine a ranar Alhamis, inda ya kira masu yin hakan “Isra’ila ’yan ta’adda.”

Wani jami’in Amurka da wani jami’in Isra’ila sun ce jami’an fadar White House na matsa wa Netanyahu ya fito fili ya yi Allah-wadai da ayyukan ‘yan share-fagen.

Jami’an sun ce Washington ta fara nuna adawa bayan ta gano cewa gidan wani Ba’amurke dan asalin Falasdine na cikin gidajen da aka kai wa hari.

Netanyahu bai yi wani bayani kan killace gidajen da ke Qusra ba, yayin da ofishinsa da fadar White House ba su mayar da martani nan take ba.

“Har yanzu ‘yan share-fagen suna nan”

Tasirin tashin hankalin da wasu ‘yan share-fagen Yahudawa ke haddasawa a Yammacin Kogin Jordan ya karu cikin shekaru uku tun bayan harin da Hamas ta jagoranta a ranar 7 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Aysha Hassan, wata Bafalasdiniya da ke zaune a daya daga cikin gidaje uku da ake killacewa, ta ce mazauna yankin na cikin tsananin tsoro.

Hassan ta ce ta ga wasu ‘yan share-fage a kusa da gidan da sanyin safiya, sannan ta aika wa Reuters bidiyon da ta dauka daga taga.

Ta ce wasu masu fafutuka daga kasashen waje da Isra’ila sun kai wa mutanen da suka makale abinci, ruwan kwalba da kayan gwangwani.

Sai dai sojojin Isra’ila sun hana masu fafutukar kai kayan tallafin kai tsaye zuwa gidajen, suna cewa yankin an rufe shi ne saboda dalilan tsaro.

Masu fafutukar sun ce sojojin sun ce za su duba kayan tallafin sannan su kai su ga iyalan da abin ya shafa.

Hassan ta ce daga bisani sojojin sun ba mazauna damar fita daga gidajensu, su dauki kayan da aka ajiye a wata hanya mai kasa, sannan su shigar da su cikin gidajensu.

Sojojin Isra’ila sun ce sun cire tanti

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Falasdinawa kusan 15, ciki har da yara biyu, sun makale a gidajensu ba tare da ruwa ko wutar lantarki ba.

Kara karanta wannan

Assma: Musulma ta yi zarra a Amurka, ta kafa tarihin zama alkali a kotu

Wani bidiyo da wani Bafalasdine da ya makale a daya daga cikin gidajen ya dauka, kuma Reuters ta samu, ya nuna wasu ‘yan share-fage bakwai a kusa da wani tanti shudi.

A cikin bidiyon, ana ganin wani mutum yana jefa duwatsu zuwa kauyen, yayin da wani kuma ya zo da kujeru.

Daga baya motocin sojojin Isra’ila da jami’an tsaro suka isa wurin, inda aka ga tantin ya rushe a kasa.

Rundunar Sojin Isra’ila ta ce wasu fararen hular Isra’ila sun kafa tanti a yankin Qusra, sannan sojojin IDF suka shiga domin cire shi tare da kare mazauna yankin.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da aka tura sojoji da dama zuwa Qusra, inda suka mamaye wasu gidajen kauyen.

Gwamnatin Netanyahu, wadda ake kallonta a matsayin gwamnatin da ta fi karkata zuwa bangaren dama a tarihin Isra’ila, ta jagoranci gagarumin fadada matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan.

Yahudawan Isra'ila sun kona masallatai a Falasdinu

A baya, an ji cewa an zargi Yahudawa 'yan share wuri zauna da kona masallatai biyu da kuma motoci da gonaki a yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

Kara karanta wannan

Sojoji da jiragen yaƙi sun zafafa hare hare, sun rutsa yan bindiga ta sama da ƙasa a jihohi 2

Hare-haren sun zo ne kwana biyu bayan wani rikici tsakanin Yahudawan da Falasɗinawa ya yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa huɗu da Isra’ilawa biyu.

Rikicin Yahudawan ya ƙara tsananta yanayin tsaro a yankin, yayin da hare-haren da ake kai wa Falasɗinawa ke ƙaruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.