'Yan Najeriya na Cikin Alheri, An Turo Musu Tallafin Fiye da Naira Biliyan 40 daga Kasar Waje
- Gwamnatin kasar China ta bai wa Najeriya tallafin Yuan miliyan 200, kwatankwacin kimanin Naira biliyan 40
- Rahoto ya nuna cewa za a yi amfani da tallafin wajen aiwatar da ayyukan da gwamnatocin kasashen biyu suka amince da su
- Kasashen biyu sun ce suna son kara zurfafa hadin gwiwar diflomasiyya da bunkasa tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin China ta yi alkawarin bai wa Najeriya tallafin yuan miliyan 200, wanda ya haura Naira biliyan 40 domin taimakawa kasar wajen aiwatar da wasu ayyukan ci gaba ga jama'arta
An bayyana hakan ne ranar Alhamis bayan da Jakadan China a Najeriya, Yu Dunhai, ya gana da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Dr Ahmed Dunoma, a Abuja.

Source: Getty Images
Leadershi ta ruwasito cewa wata sanarwa da Ofishin Jakadancin China a Najeriya ya fitar ta ce tallafin na daga cikin matakan karfafa alakar diflomasiyya da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
China ta dauko tarihin shekaru 55
Jakadan Yu ya ce a cikin shekaru 55 da suka gabata tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin China da Najeriya, kasashen biyu sun kasance cikin sahun gaba wajen karfafa dangantakar China da kasashen Afirka.
Ya ce a shekarun baya-bayan nan, karkashin jagorancin Shugaban China, Xi Jinping, da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta shiga wani sabon mataki na ci gaba mai inganci.
A cewarsa, China da Najeriya sun ci gaba da tuntubar juna tare da aiki tare wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
Abubuwan da za a yiwa yan Najeriya
Jakadan China ya ce:
“Domin kara tallafa wa ci gaban kasa da bunkasar tattalin arzikin Najeriya, China za ta samar da tallafin yuan miliyan 200 ga Najeriya domin aiwatar da ayyukan da gwamnatocin kasashen biyu suka amince da su.”
Ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin China na kara tallafa wa Najeriya wajen cimma manufofin ci gabanta da bunkasa tattalin arzikinta.
Najeriya ta yaba wa China
A nasa bangaren, Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Dr Ahmed Dunoma, ya yabawa China kan irin tallafin da take bai wa Najeriya wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Dunoma ya ce tallafin ya nuna irin nauyin da China ke dauka a matsayin babbar kasa, sannan ya kara tabbatar da zurfin zumunci da ke tsakanin Najeriya da China.

Source: Getty Images
Ya tabbatar da cewa Najeriya za ta yi amfani da tallafin yadda ya kamata tare da yin aiki da China wajen aiwatar da yarjejeniyoyin hadin gwiwar kasashen biyu.
Ya ce hakan zai kara karfafa zumunci tsakanin Najeriya da China tare da samar da karin alfanu ga al’ummomin kasashen biyu.
Najeriya da China sun sabunta yarjejeniya
Kun ji cewa gwamnatin Najeriya da Kasar China sun sabunta yarjejeniyar kudi wanda darajarta ta kai Yuan biliyan watau dala biliyan 2.
An yi wannan ne da nufin bunkasa kasuwanci da alakar da ke tsakanin Najeriya da ke Afrika ta yamma da kasar da ke Asiya.
Yarjejeniyar ta ba da damar a rika ciniki tsakanin kasashen biyu da kudin Naira da Yuan, wannan zai sa a huta da wahalar Dala.
Asali: Legit.ng

