Hukumar DSS Ta Sake Gurfanar da El Rufai, Yana Fuskantar Sababbin Tuhume Tuhume
- Hukumar DSS ta sake gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a kotun tarayya da ke Abuja kan sababbin tuhume-tuhume
- Jami’an DSS sun killace harabar kotu tare da hana jama’a shiga, lamarin da ya jawo Omoyele Sowore ya jagoranci wata karamar zanga zanga
- El-Rufai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da DSS ke yi masa ciki har da zargin sauraren wayar mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar tsaro ta DSS ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
DSS ta sake gurfanar da Malam Nasir El-Rufai ne bisa wasu sababbin tuhume-tuhume da suka shafi datsar wayar mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.

Source: Twitter
DSS ta sake gurfanar da El-Rufai a kotu
An kawo El-Rufai harabar kotun da misalin karfe 8:55 na safiyar ranar Litinin karkashin tsauraran matakan tsaro daga jami’an DSS masu dauke da makamai, in ji rahoton Daily Trust.
A safiyar Litinin ɗin nan ne jami’an DSS suka ɗauko El-Rufai da ke tsare a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, inda yake fuskantar zargin badaƙalar kuɗaɗe a lokacin mulkinsa.
Wani jami’in Hukumar ICPC ya shaida wa Aminiya cewa tun da misalin ƙarfe 7:00 na safe jami’an Hukumar DSS suka je suka ɗauke shi domin kai shi kotu.
Jami’an DSS sun kawo shi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin gurfanar shi kam zargin tatsar bayanai da daga wayar Malam Nuhu Ribadu.
Majiyar ICPC ta ce:
“Eh, karar da ake yi yanzu ba tamu ba ce. Jami’an DSS sun zo tun da sassafe suka tafi da shi domin gurfanar da shi a kotu.”
Sowore ya jagoranci zanga-zanga
Jami’an tsaron sun killace harabar kotun tare da hana ‘yan jarida, ma’aikata da sauran jama’a shiga na wani lokaci, lamarin da ya haifar da takaddama da gajeriyar zanga-zanga.
Dan gwagwarmaya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore, ya jagoranci wata gajeriyar zanga-zanga a harabar kotun.
Sowore ya ce kotu wuri ne na jama’a, saboda haka bai kamata a hana ‘yan Najeriya shiga domin kallon yadda ake gudanar da shari’a ba.

Source: Facebook
El-Rufai ya musanta tuhume-tuhumen DSS
Makonni uku da suka gabata, da aka gurfanar da El-Rufai gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik, ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, in ji rahoton Business Day.
Lauyan DSS, Oluwole Aladedoye SAN, ya sanar da kotu cewa an shigar da sabuwar takardar kara mai dauke da tuhume-tuhume guda biyar a ranar 13 ga Afrilu domin maye gurbin tsohuwar takardar kara mai tuhume-tuhume uku.
Lauyan El-Rufai, Oluwole Iyamu SAN, bai yi adawa da bukatar ba, wanda hakan ya sa kotu ta soke tsohuwar karar tare da amincewa da sabuwar.
Bayan an karanta sabuwar karar a gabansa, El-Rufai ya sake bayyana cewa ba shi da laifi a kan dukkan tuhume-tuhumen.
Kotu ta bada belin El-Rufai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan N100m tare da sharudda masu tsauri.

Kara karanta wannan
Kotu ta yanke wa Halima Umar hukunci bayan kama ta da makamai masu hadari a Filato
Kotu ta umarci El-Rufai ya rika zuwa hedikwatar hukumar DSS duk ranar Juma’ar karshen wata domin sanya hannu yayin da ake ci gaba da shari’a.
Kotun ta kuma ce dole ne wanda zai tsaya wa tsohon gwamnan ya kasance babban ma’aikacin gwamnati mai gida a Maitama ko Asokoro.
Asali: Legit.ng

