Abuja
Shaidar gwamnati ta fada wa kotun tarayya da ke Abuja cewa wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulki sun bayar da bayanansu cikin son rai ba tare da tilastawa ba.
Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Tinubu kan mutuwar Hon. Abba Anas Adamu a hannun masu garkuwa ranar 12 ga Mayu, 2026, yana mai kiran a gyara tsaro da gaggawa.
Ministocin Najeriya da Maroko sun tattauna kan aikin bututun iskar gas na NMGP a ranar 10 ga Mayu, 2026, inda ake sa ran Tinubu zai sanya hannu a ƙarshen shekara.
Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya sanar da cewa APC za ta yi zaben fitar da gwani na ƙato bayan ƙato idan har masu neman takara ba su yarda da sulhu ba.
Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, bai halarci tantancewar APC ba yayin da jam’iyyar ta tantance gwamnoni 14 da sauran masu neman mukaman zaben 2027.
A labarin nan, za a ji cewa duk da rigingimun shugabanci da ya dabaibaye wani sashe na APC, jam'iyyar tana cinikin fam har ta tara sama da N4bn gabanin 2027.
Kwamitin tantancewa karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya fara tantance gwamnoni da sauran yan takara a Abuja.
Tsagin da jam'iyyar ADC da Nafiu Bala ke jagoranta ya bayyana cewa bai kamata jam'iyyar ta fara sayar da fom din neman takara ba. ya bukaci David Mark ya dakata.
Babban rikici ya raba kan Gwamnonin APC (PGF) a ranar 8 ga Mayu, 2026, inda aka samu ɓangarori biyu ƙarƙashin Hope Uzodimma da Dapo Abiodun gabanin zaɓen 2027.
Abuja
Samu kari