Yan Bindiga Sun Dana Tarko a cikin Dare, Sun Rutsa Wasu Mutane da ke Hanyar zuwa Abuja

Yan Bindiga Sun Dana Tarko a cikin Dare, Sun Rutsa Wasu Mutane da ke Hanyar zuwa Abuja

  • Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 14 da ke tafiya daga Enugu zuwa babban birnin tarayya Abuja
  • Rahotanni daga Rundunar ’Yan sanda sun nuna cewa dakarun tsaro sun ceto biyar daga cikinsu, ciki har da yaro mai shekara hudu
  • Rundunar ta bayyana cewa a halin yanzu mutum tara na ci gaba da kasancewa a hannun wadanda ake zargi sun yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue, Nigeria - Akalla fasinjoji 14 da suka taso daga jihar Enugu zuwa Abuja sun fada hannun ’yan bindiga a yankin Ankpechi–Omutele da ke karamar hukumar Ohimini a jihar Benue.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis, lokacin da fasinjojin ke cikin wata motar haya yayin da ’yan bindigar suka tare motar tare da tafiys da fasinjojin cikin jeji.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama fasto da ya kulla sace matan wasu malaman addini a Plateau

Taswirar jihat Benuwsi.
Taswirar jihar Benue da ke Arewa ta Taskiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

’Yan sanda sun ceto mutum 5

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue, DSP Orchia Peter Aondongu, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutum biyar daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su. Ya ce wadanda aka ceto sun hada da wani yaro dan shekara hudu.

A cewar Aondongu, mutum tara na ci gaba da kasancewa a hannun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Ya ce rundunar ta kaddamar da aikin ceto da sanyin safiyar Juma’a, tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro.

Jami'an tsaro sun gwabza da maharan

Aondongu ya ce aikin ceton ya kai ga musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da masu garkuwa da mutanen, kafin a samu damar kubutar da wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce:

“Aikin ceton ya haifar da musayar wuta, kuma an yi nasarar ceto mutum biyar, ciki har da yaro dan shekara hudu, yayin da mutum tara ke ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da su.”

Kara karanta wannan

Miyagu daga kabilar Tibi sun hallaka direban Dangote da wata mata a Benue

Ya kara da cewa daya daga cikin wadanda aka ceto ya samu raunin harbin bindiga a yayin aikin, yana mai cewa an garzaya da wanda ya samu raunin zuwa wata cibiyar lafiya da ke Otukpo.

Yan sanda na kokarin ceto sauran

Kakakin ’yan sandan ya ce jami’an rundunar, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, na kara kaimi wajen ganin an ceto sauran mutum tara cikin koshin lafiya.

Ya ce jami’an na gudanar da aikin cikin taka-tsantsan, inda lafiyar fasinjojin da aka yi garkuwa da su ta kasance babban abin da ake bai wa fifiko, kamar yadda Punch ta rahoto.

Yan sanda.
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Benue, CP Cletus Nwadiogbu, ya bayyana damuwarsa kan halin da iyalan wadanda lamarin ya shafa da sauran jama’a ke ciki.

Ya tabbatar musu cewa ana daukar matakan da suka dace domin ganin an sako wadanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutanen cikin aminci.

Yan bindiga sun sace basarake a Neja

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake, Mallam Abubakar Lafiya mai shekaru 90 a duniya a jihar Neja.

Mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa wadanda suka kai harin sun mamaye gidanNbasaraken ne kafin su yi awon gaba da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262