Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aliyu Ladan Ya Rasu
- An sanar da rasuwar Sheikh Imam Aliyu Ladan, wani malamin addinin Musulunci da ya shahara wajen karatun Alƙur’ani da ilimin Hadisi
- Dr Abdullahi Lamido ya bayyana marigayin a matsayin ɗan uwansa kuma malaminsa da Allah ya ba wa Alƙur’ani da kyakkyawar mu’amala
- Malaman addini da ɗalibai sun yi ta’aziyya tare da roƙon Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An sanar da rasuwar Sheikh Imam Aliyu Ladan, wani malamin addinin Musulunci da ya shahara wajen karatun Alƙur’ani a Arewacin Najeriya.
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya, lamarin da ya jawo ta’aziyyar malamai da ɗalibansa.

Source: Facebook
Dr Lamido ya yi ta’aziyya
Dr Abdullahi Lamido ya sanar da rasuwar a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana Sheikh Aliyu Ladan a matsayin ɗan uwansa kuma malaminsa.
Ya ce marigayin malami ne wanda Allah Ya ba shi wa Alƙur’ani, kuma ya karanci ilimin Hadisi a Jami’ar Musulunci ta Madina.
Dr Abdullahi ya ce Allah Ya ba wa marigayin natsuwa, haƙuri da kyakkyawar mu’amala da mutane.
Ya kuma bayyana yadda suke ƙoƙarin kwaikwayon karatun Alƙur’aninsa tun suna ƙanana saboda irin sautin da Allah Ya ba shi wajen karatu.
Ya ce:
“Allah ya jikan Sheikh Aliyu Ladan ya sanya Firdausi makomarsa.”
Sulaiman Lawal Sule ya yi ta’aziyya
Sulaiman Lawal Sule ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin malamansa, yana mai cewa Sheikh Aliyu Ladan ya rasu bayan fama da jinya.
Ya roƙi Allah Ya yafe masa kura-kurensa, Ya tabbatar da shi wajen amsa tambayoyin kabari, sannan Ya albarkaci iyalansa da zuriyarsa.
A sakon da ya wallafa a Facebook, Sulaiman ya kuma mika ta’aziyyarsa ga dukkan malamai da ɗaliban Riyadhul Qur’an, musamman Sheikh Yakubu Musa Hassan da sauran malamai da ‘yan uwa.
Sakon ta'aziyyar da aka fitar
Sulaiman A. Musa ya bayyana alhini kan rasuwar, yana mai roƙon Allah Ta’ala Ya yi wa marigayin rahama Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa.
Abbas Mohammed Bose ya roƙi Allah Ya jiƙan marigayin da rahama, Ya gafarta masa kura-kurensa, Ya kuma sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.
Samaila Ali ya ce:
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Allah Ya jiƙansa, Ya masa rahama, Ya kyautata ƙarshenmu gaba ɗaya.”
Har yanzu Legit Hausa ba ta samu cikakken bayani kan lokaci da wurin da za a gudanar da jana’izar Sheikh Imam Aliyu Ladan ba.
Al-Issa ya gana da Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi Sakataren Ƙungiyar Malaman Musulmi ta Duniya, Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Sheikh Al-Issa ya jagoranci tawaga da ta kai wa shugaban ƙasar ziyarar ban girma, tare da Jakadan Saudiyya a Najeriya, Dr Yakubu Gambo, da shugaban ƙasa na JIBWIS, Sheikh Bala Lau.
Ziyarar ta haɗa shugaban ƙasa da manyan malaman Musulunci domin ƙarfafa hulɗa da tattaunawa tsakanin hukumomi da ƙungiyoyin addini.
Asali: Legit.ng

