"Ku Tashi Tsaye Ku Kare Kan Ku daga Ƴan Bindiga," Hadimin Tinubu ga Ƴan Najeriya

"Ku Tashi Tsaye Ku Kare Kan Ku daga Ƴan Bindiga," Hadimin Tinubu ga Ƴan Najeriya

  • Daniel Bwala ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba jama’a damar kare kansu idan suka fuskanci hari ko barazanar rasa rayuwa
  • Mai ba shugaban kasa shawara ya bayyana hakan ne bayan hare-haren da aka kai a Oyo da kuma sace malamai da dalibai
  • Bwala ya ce duk da akwai dokar kare kai, dole sai an nemi amincewar gwamnati kafin ya iya mallakar wasu makamai da amfani da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan sadarwa, Daniel Bwala, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a fadin kasar nan.

Daniel Bwala ya bayyana cewa kundin tsarin mulki ya ba ‘yan Najeriya damar kare kawunansu a duk lokacin da suke fuskantar hare-haren 'yan bindiga ko cikin wani hadari.

Kara karanta wannan

Majalisar Amurka ta shirya kawo wa Trump cikas game da yaki da kasar Iran

Daniel Bwala ya ce 'yan Najeriya na da 'yancin kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga.
Daniel Bwala tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa Abuja. Hoto: @BwalaDaniel
Source: Twitter

Hadimin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News a ranar Laraba, 20 ga Mayun 2026.

“Kowa na da damar kare kansa” - Bwala

Kalaman nasa sun zo ne bayan hare-haren da aka kai a yankin Esiele da ke karamar hukumar Orire ta jihar Oyo da kuma sace malamai da dalibai a makarantar firamare ta LA.

“Kundin tsarin mulki ya tabbatar wa kowane dan Najeriya da damar kare kansa; kana da damar kare kanka,” in ji Daniel Bwala.

Ya kara da cewa idan aka hada hakkin mutum daya da na sauran jama’a, hakan na zama hakkin hadin gwiwa wajen kare kai daga masu aikata laifuffuka.

Bwala ya bayyana cewa idan wani ya shiga gidan mutum da niyyar kashe shi, dokar kasa ta amince mutum ya kare kansa ta kowace hanya mai yiwuwa.

“Idan wani ya zo gidana domin kashe ni, zan iya daukar duk wani makami da zan yi amfani da shi wajen kare kaina, kundin tsarin mulki ya ba ni dama"

Kara karanta wannan

Sojojin Amurka sun kai hari Najeriya, Trump ya ce an kashe Abu Bilal al Minuki

- Daniel Bwala

Martanin Bwala kan mallakar makamai

Sai dai Bwala ya bayyana cewa akwai dokoki da ke tsara yadda jama’a za su mallaki makamai musamman bindigogi.

Ya ce ba kowane makami ne jama’a za su iya mallaka ba tare da amincewar gwamnati ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya kara da cewa jama’a na iya hada kai su nemi gwamnati ta ba su damar tsara hanyoyin kare kansu cikin tsarin doka.

Daniel Bwala ya bayyana cewa akwai makamai, musamman bindigogi da sai an nemi izini za a yi amfani da su.
Daniel Bwala, mai ba shugaban kasa shawara kan sadarwa a bangaren manufofin gwamnati. Hoto: @BwalaDaniel
Source: UGC

Bwala ya yi magana kan rashin tsaro

Da yake magana kan matsalar tsaro gaba daya, Daniel Bwala ya bayyana cewa aikata laifuffuka matsala ce da ake fama da ita a kasashe daban-daban na duniya.

A cewarsa, babu wata gwamnati da za ta iya kawo karshen matsalar rashin tsaro ita kadai ba tare da hadin kan jama’a ba.

“Abin da muke nema shi ne mafita; mugayen mutane suna ko’ina a duniya duk kuwa yadda gwamnati ta tsaurara matakai,” in ji Bwala.

Kara karanta wannan

Yahudawa sun bankawa masallaci, motoci wuta yayin ibada a Isra'ila

Ya ce yana fahimtar damuwar ‘yan Najeriya kan yawaitar hare-hare da kashe-kashe, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da kokarin magance matsalar.

Gwamna ya ce mutane su kare kan su

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Dikko Radda ya shawarci jama'ar jihar Katsina da su tashi su kare kawunansu daga hare-haren 'yan bindiga.

Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa za ta ba kowanne gari duk wata gudunmawa da yake bukata wajen yin hakan ta hanyar da ta dace.

Mai girma gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da makarantun Islamiyya guda uku da wani ya gina a Malumfashi da Mani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com