Tsagin Jam’iyyar Adawa Za Ta Yi Bazata, Kowa Zai Samu Fom Din Takara Kyauta
- abureTsagin jam’iyyar LP a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ta sanar da cewa za ta shiga zaɓen 2027 da ake tunkara
- Abure ya ce tsaginsu ya ɗaukaka ƙarar kotun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli, yana mai jaddada cewa shi ne halastaccen shugaban LP.
- Shugaban ɓangaren LP ɗin ya zargi wasu jiga-jigan siyasa da ƙoƙarin raunana jam’iyyar bayan nasarar da ta samu a zaɓen shekarar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ɓangaren jam’iyyar Labour Party ƙarƙashin jagorancin Barista Julius Abure ya bayyana cewa zai shiga zaɓen 2027 gaba ɗaya tare da bayar da fom kyauta.
Sanarwar ta zo duk da cewa jam’iyyar LP ta riga ta bayyana kuɗaɗen fom ga masu neman takara daban-daban a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

Source: Twitter
Kudin fom na LP da aka fitar tun farko

Kara karanta wannan
Obi: NDC ta rufe sayar da fam, ta samar da 'dan takarar shugaban kasa 1 gabanin 2027
Daily Trust ta rawaito cewa jam’iyyar ta sanya fom ɗin majalisar dokoki ta jiha kan Naira miliyan uku, yayin da na tarayya ya kai miliyan biyar.
Jam’iyyar ta kuma sanya fom ɗin takarar majalisar dattawa kan Naira miliyan 10, yayin da na gwamna ya kai Naira miliyan 25.
Haka kuma, tikitin takarar shugaban ƙasa ya kai Naira miliyan 50, inda fom ɗin nuna sha’awa ya kai miliyan 10 da na takara miliyan 40.
Abure ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a Abuja, inda ya musanta zargin neman kuɗi daga gwamnan Abia, Alex Otti, yayin sulhu.
Ya ce tattaunawar sulhun ta ta’allaka ne kawai kan rabon iko da tsarin shugabanci a cikin jam’iyyar ba tare da maganar kuɗi ba.
Wannan rikici ya biyo bayan shari’ar shugabancin jam’iyyar da ta ƙara tsananta rabuwar kai da rashin tabbas gabanin zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

Source: Twitter
Yaushe za a yi zaben fitar da gwani?
Abure ya ce wannan ne karon farko da yake magana bayan hukuncin kotun, yana mai cewa suna jiran tattara bayanan shari’ar gaba ɗaya.

Kara karanta wannan
Yan Kwankwasiyya, Obidents sun shirya tara miliyoyi saboda takarar Obi, Kwankwaso
Shugaban ɓangaren ya ce shugabancin da yake jagoranta ya samo asali ne daga babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Nnewi a 2024, cewar Punch.
Ya ƙara da cewa duk da hukuncin kotu, ɓangarensa zai gudanar da zaɓen fitar da gwani da tsarin zaɓen ’yan takara na shekarar 2027.
A cewarsa, za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na gwamnoni da ’yan majalisar jiha a ranar 27 ga Mayu na shekarar 2026.
Ya kuma ce zaɓen fitar da gwani na majalisar tarayya zai gudana a ranar 29 ga Mayu, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓe.
NDC ta tsayar da sayar fom din takara
Kun ba ku labarin cewa jam’iyyar hamayya a Najeriya ta NDC ta rufe sayar da fam na neman takarar shugaban ƙasa na babban zaben 2027 da ke tafi.
Rahotanni sun nuna cewa Peter Obi ne kaɗai ya sayi fam ɗin takarar shugaban ƙasar, wanda ke nufi shi ne zai fafata da Bola Tinubu.
Jam’iyyar ta ƙara wa’adin sauran kujeru kamar gwamnoni da majalisu da mako guda yayin da harkokin siyasa suka kankama.
Asali: Legit.ng