Tirkashi: Wasu Mutane Sun Fadawa Tinubu Cewa Shettima na Shirin Kashe Shi
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce wasu mutane sun fada wa Shugaba Bola Tinubu cewa yana shirin kashe shi domin karbar mulki
- Shettima ya bayyana cewa mutanen da suka kai korafin sun fito ne daga jihar Borno, watanni uku kacal bayan sun shiga mulki a 2023
- Mataimakin shugaban kasar ya yaba wa Tinubu bisa rashin yarda da zargin tare da kira ga ‘yan Najeriya su guji haddasa rarrabuwar kawuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana yadda wasu mutane suka yi kokarin haddasa sabani tsakaninsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, watanni uku bayan sun shiga mulki.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban mulkin soja, Janar Yakubu Gowon mai suna “My Life of Duty and Allegiance.”

Kara karanta wannan
Mutane sun barke da dariya da Jonathan ya kira Sarkin Kano Sanusi II da wani suna a taro

Source: Twitter
“Sun ce zan kashe Tinubu” - Shettima
A cewarsa, watanni uku bayan shigarsu mulki, wasu mutane daga jihar Borno sun je wajen shugaban kasa, inda suka ce yana shirin kashe shi domin karbar mulki, in ji rahoton Daily Trust.
Shettima ya ce shugaban kasa ya kira shi domin sanar da shi abin da aka fada masa.
Ya ce:
“Watanni uku bayan an rantsar da mu, wasu mutane sun gaya wa Tinubu cewa ina shirin kashe shi domin in karbi mulki.”
Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa shugaban kasar ya fada masa yadda mutanen suka nemi ya daina sanya wasu kaya da Shettima ya ba shi.
A cewarsa:
“Shugaban kasa ya kira ni ya ce, ‘Zauna! Mutanenka sun zo sun ce in daina sanya kayan Shettima.’”
Tinubu bai yarda da zargin ba
Shettima ya ce shugaban kasar ya nuna cewa zargin ba shi da tushe saboda kayan da ake magana a kai tun kafin zaben shugaban kasa aka ba shi.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun far wa mutane bayan sun dawo daga sayayyar kayan Sallah a Katsina
Ya ce Tinubu ya fada masa:
“Lokacin da ka ba ni kayan nan, ni mai neman takara ne kawai. Ban ma zama dan takarar jam’iyya ba a lokacin, kai ma ba ka zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ba.”
Shettima ya ce duk da korafin da aka kai, Tinubu ya ci gaba da sanya kayan saboda ba ya yarda da tsafe-tsafe ko camfi.
Shettima ya yi kira ga hadin kai
Mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi hadin kai maimakon yada rarrabuwar kawuna a tsakanin mutanen da suka ga suna da aminci da juna.
Ya ce ya kamata mutane su zama masu taimakon juna da kare martabar ‘yan uwansu maimakon kokarin haddasa rikici da gaba a tsakanin shugabanni da jama’a.

Source: Twitter
An musanta sabanin Tinubu da Shettima
A baya bayan nan an samu rahotanni da ke nuna cewa akwai sabani tsakanin Tinubu da Shettima, amma fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin, in ji rahoton Vanguard.
Mai taimaka wa Shettima kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha, ya bayyana cewa babu wani mataimakin shugaban kasa da ya taba samun cikakken goyon bayan shugaban kasa kamar Shettima.
“A cikin siyasar Najeriya, Kashim Shettima ya nuna aminci da biyayya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Hakan ya nuna kyakkyawar hadin kai da fahimtar juna a gwamnatin nan.”
- Stanley Nkwocha.
Martanin APC kan alakar Tinubu, Shettima
A wani labari, mun ruwaito cewa, jam’iyyar APC mai mulki ta musanta ikirarin cewa akwai sabani tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.
Haka kuma, jam’iyyar ta yi watsi da jita-jitar cewa Tinubu yana shirin sauya mataimakinsa kafin zaben 2027.
Daraktan yada labaran APC na kasa, Bala Ibrahim, ya ce rahotannin da ke cewa ana shirin sauya Kashim Shettima a matsayin mataimakin Tinubu a ba shi da tushe.
Asali: Legit.ng
