Ojukwu, Sojan da Ya Shigo da Makamai Aka Kashe Miliyoyin Ƴan Najeriya a Mulkin Gowon
- Tsohon shugaban mulkin soja Yakubu Gowon ya ce an shigo da makamai daga kasashen ketare zuwa yankin Gabas kafin yakin basasar Najeriya
- Gowon ya yi zargin cewa Chukwuemeka Ojukwu ya yi amfani da taron Aburi wajen neman lokaci domin tara makamai da shirya lokacin yakin Biafra
- Tsohon shugaban kasar ya ce duk da ikirarin Ojukwu na cewa Gabas ta kawo karfi a makamai, gwamnatin tarayya ta fi yankin karfin soji a lokacin yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana yadda aka shigo da makamai da harsasai daga wasu kasashen ketare zuwa yankin Gabashin Najeriya kafin barkewar yakin basasa.
Gowon, wanda ya mulki Najeriya daga 1966 zuwa 1975, ya ce akwai damar kauce wa yakin basasar da aka shafe watanni 30 ana gwabzawa, wanda ya jawo asarar rayukan miliyoyin 'yan kasa.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Source: Getty Images
Yakubu Gowon ya tuno yakin basasar Najeriya
A cewar Gowon, hakan zai yiwu da tsohon shugaban yankin Gabas, Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, ya mutunta yarjejeniyar taron Aburi da aka gudanar a Ghana a Janairun 1967, in ji rahoton Premium Times.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihinsa mai suna My Life of Duty and Allegiance wanda aka kaddamar a Abuja ranar Talata.
Gowon ya ce Ojukwu ya nemi lokaci ne domin tara makamai da harsasai kafin barkewar yakin Biafra
A cikin littafin, Gowon ya ce ya yi kokarin sasanta rikicin ta hanyar tattaunawa da Ojukwu, amma shugaban yankin Gabas ya ki amincewa da fita daga yankinsa saboda dalilan tsaro.
Ya ce hakan ne ya sa shugaban kasar Ghana na lokacin, Joseph Ankrah, ya shirya taron sulhu tsakanin bangarorin biyu a Peduase Lodge da ke Aburi a Ghana.
Dabarar Ojukwu ta shigo da tarin makamai
Gowon ya bayyana cewa Ojukwu ya gabatar da wasu sharudda da suka fi dacewa da bukatun yankin Gabas, ciki har da kin amfani da karfi wajen warware rikicin.
Sai dai ya yi zargin cewa manufar hakan ita ce neman karin lokaci domin tara makamai da harsasai kafin fara yaki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ya ce:
“Mun san yana neman karin lokaci ne saboda shirinsa na tara makamai ya samu tangarda bayan wani jirgin DC-4 dauke da makamai ya fadi a tsaunukan Arewacin Kamaru a watan Oktoban 1966.”
Gowon ya ce daga baya Ojukwu ya tabbatar musu da zargin tara makamai yayin wata ganawa da kwamitin sulhu na kasa a Enugu a watan Mayun 1967.

Source: Twitter
Ikirarin Ojukwu na karfin Gabas a makamai
A cewarsa, Ojukwu ya bayyana cewa yankin Gabas ya kai matsayin “samun daidaiton makamai” wanda zai ba su damar tattauna makomar Najeriya ta fuskar amfani da karfin bindiga.
Gowon ya ce Ojukwu ya yi ikirarin cewa:
“A Gabas muna da rundunar soja mafi girma a nahiyar Afrika.”
Sai dai Gowon ya ce bai yarda da wannan ikirari ba, yana mai cewa gwamnatin tarayya na da rinjaye ta fuskar sansanonin soja da yawan dakarun yaki.

Kara karanta wannan
Mutane sun barke da dariya da Jonathan ya kira Sarkin Kano Sanusi II da wani suna a taro
Yadda aka yi wa Gowon juyin mulki
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana yadda wasu jami’an da ya amince da su suka kifar da gwamnatinsa a 1975.
Gowon ya ce tsohon kwamandan tsaron fadarsa, Joseph Garba, da wasu jami’ai na cikin wadanda aka sanar masa sun shirya juyin mulkin.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana yadda ya samu labarin hambarar da gwamnatinsa yayin taron OAU a Uganda daga bakin Shugaba Idi Amin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
