Assma: Musulma Ta Yi Zarra a Amurka, Ta Kafa Tarihin Zama Alkali a Kotu

Assma: Musulma Ta Yi Zarra a Amurka, Ta Kafa Tarihin Zama Alkali a Kotu

  • An samu ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan nadin wata Musulma, Assma Ali, a matsayin alƙalin birni a wani ƙaramin gari a jihar Mississippi ta Amurka
  • Wasu ‘yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta sun kai mata hari saboda addininta, tare da zargin za ta kafa Shari’a ba tare da gabatar da wata hujja ba
  • Sai dai masana shari’a da mutanen da suka san Ali sun bayyana cewa ƙwararriyar lauya ce kuma ta cancanci matsayin da aka naɗa ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Mississippi – An yi ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan an naɗa wata lauya Musulma, Assma Ali, a matsayin alƙalin birnin Benoit da ke jihar Mississippi ta Amurka.

Ali, wadda Ba’amurkiya ce ‘yar asalin Yemen, an naɗa ta a makon da ya gabata a matsayin alƙalin birnin da ke da mutane kasa da 400 a gundumar Bolivar.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama fasto da ya kulla sace matan wasu malaman addini a Plateau

Assma Ali a wani taro
Assma Ali da ta zama alkali a Amurka. Hoto: Assma Ali
Source: Facebook

Rahoton Mississippi Free Press wasu ‘yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta sun soki nadin nata saboda addininta, duk da cewa ba su gabatar da wata hujja da ke nuna rashin cancantarta ba.

Masana sun kare Assma Ali

Lauya kuma farfesa a Makarantar Shari’a ta Jami'ar Kiristoci ta Mississippi, Frank Rosenblant, ya ce hare-haren da ake kai wa Ali sun samo asali ne daga addininta.

Rahoton ABC ya ce lauyan ya nuna cewa wasu mutane daga wajen jihar sun ga mace sanye da hijabi ne kawai, sannan suka fara neman a ɗauki mataki a kanta.

Rosenblatt, wanda ya san Ali tsawon shekaru, ya kuma yaba mata kan yadda take taimaka wa matasa lauyoyi wajen samun ƙwarewa.

Ya bayyana cewa Kundin Tsarin Mulkin Amurka da na Mississippi sun haramta hana mutum riƙe mukamin gwamnati saboda addininsa.

Assma Ali ta bayyana matsayarta

Ali, wadda ke da kusan shekaru 10 tana aikin lauya, ta ce za ta yi aiki ne bisa Kundin Tsarin Mulkin Amurka da dokokin jihar Mississippi.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Bugu da kari, Assma ta ce za ta gudanar da aikinta cikin adalci, gaskiya, rashin son rai da mutunta doka.

Ali ta kuma wallafa rantsuwar kama aiki da kuma ajandar taron majalisar birnin Benoit da ke nuna cewa an amince da nadin nata domintabbatar da adalci.

Ta yi digiri a fannin shari’a a kwalejin Mississippi a 2017, wanda a yanzu ake kira jami'ar Kiristoci ta Mississippi, kuma a wannan shekarar aka shigar da ita cikin ƙungiyar lauyoyin jihar.

Sikeli da ake gudanar da aiki da shi a kotu
Abubuwan da ke nuna alamun shari'a a kotu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Aikin alƙalan birane a Amurka

A Mississippi akwai sama da alƙalan birane 200, wadanda hukumomin biranen ke naɗawa ba gwamnatin jihar ba.

Alƙalan suna da ikon shari’a ne kawai a cikin biranen da aka naɗa su, inda suke kula da laifuffukan karya dokokin birni, hanya, ƙananan laifuffuka da wasu shari’o’i.

Leavitt za ta yi murabus

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, za ta bar mukaminta kafin ƙarshen watan Agusta.

Kara karanta wannan

Amurka ta nuna ba daga kafa, ta caccaki Isra'ila kan taba kawayen Iran a Lebanon

Trump ya ce Leavitt za ta bar aikin ne domin ta samu ƙarin lokaci tare da ƙananan ‘ya’yanta da sauran iyalanta.

Ya kuma ce za ta zama ɗaya daga cikin manyan masu ba shi shawara, tare da taimaka wa jam’iyyar Republican wajen tunkarar zaɓen watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng