Danjuma, Dangote, BUA Sun Yi Gasar Kudi a Wani Babban Taro da Aka Shirya a Abuja

Danjuma, Dangote, BUA Sun Yi Gasar Kudi a Wani Babban Taro da Aka Shirya a Abuja

  • Tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Danjuma ya bayar da gudunmawar Naira biliyan uku wajen kaddamar da littafin tarihin Yakubu Gowon
  • Shi ma attajirin Afrika, Aliko Dangote, ya bayar da Naira miliyan 500 domin sayen kwafi 25 na littafin tarihin tsohon shugaban kasar
  • Kashim Shettima da manyan jami’an gwamnati da na soja sun halarci taron kaddamar da littafin da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Danjuma mai ritaya, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan uku yayin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon mai ritaya.

Rahoto ya nuna cewa shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, shi ma ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 500 wajen tallafa wa taron kaddamar da littafin.

Kara karanta wannan

Mutane sun barke da dariya da Jonathan ya kira Sarkin Kano Sanusi II da wani suna a taro

Danjuma, Dangote, sun ba da gudunmawar makudan kudade a bikin kaddamar da littafin Gowon.
Hagu zuwa dama: Tony Elumelu, Abdul Samad Rabiu da Aliko Dangote a taron kasuwanci na UAE-Afrika. Hoto: @asr_rabiu
Source: Twitter

An kaddamar da littafin rayuwar Yakubu Gowon

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an gudanar da bikin gabatar da littafin mai taken “My Life of Duty and Allegiance” ne a birnin tarayya Abuja.

Littafin ya kunshi babi 20 tare da halartar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda rahoton ya nuna.

Rahotanni sun nuna cewa manyan jami’an gwamnati, jakadu, manyan hafsoshin soja da sauran manyan baki sun halarci bikin da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Danjuma, wanda shi ne babban mai gabatar da littafin, ya samu wakilcin tsohon babban hafsan tsaro, Janar Martin Luther Agwai mai ritaya.

Baya ga bayar da kudin tallafi, Danjuma ya umurci a sayi kwafe 12 na littafin domin rabawa dakunan karatu na jami’o’i 20 da suka taba bai wa Gowon digirin girmamawa.

TY Danjuma ya yabawa Gowon

A jawabin da aka karanta a madadinsa, Danjuma ya bayyana Janar Yakubu Gowon a matsayin daya daga cikin manyan dattawan Najeriya da suka yi fice a duniya.

Kara karanta wannan

El Rufai: Kotu ta bada belin tsohon gwamnan Kaduna, ta kafa sharuda masu tsauri

Ya ce Gowon ya taka muhimmiyar rawa wajen hana Najeriya tarwatsewa a lokacin yakin basasa, yana mai cewa:

“Janar Gowon ba sanannen suna ba ne kawai a Najeriya, shi babban jagora ne da duniya ta amince da shi saboda kwarewa wajen shugabanci da gina kasa.”

Aliko Dangote ya bayar da N500m

Wakilin Aliko Dangote, Mansur Ahmed, ya bayyana cewa attajirin ya sayi kwafi 25 na littafin kan Naira miliyan 500 domin girmama Gowon.

Ahmed ya ce Dangote yana dan shekara 10 ne kawai lokacin da Gowon yake shugabantar Najeriya a lokacin mawuyacin hali.

Ya bayyana cewa kokarin Gowon na tabbatar da hadin kan Najeriya ne ya samar da yanayin da ya bai wa Dangote damar gina babbar daular kasuwanci a Afrika.

BUA ya sayi wasu kwafi na littafin Gowon a kan N25m
Tsofaffin shugabannin Najeriya da sarkin Musulmi, da Shettima a taron kaddamar da littafin rayuwar Gowon. Hoto: @stanleynkwocha_/X
Source: Twitter

BUA da sauran attajirai sun tallafa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sauran attajirai da manyan baki da suka halarci tron sun sayi kwafin littafin da makudan kudade.

Daga ciki akwai shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, wanda ya sayi kwafi na Naira miliyan 25.

Kara karanta wannan

APC: Akpabio, Barau Jibrin da gwamnoni 7 za su fafata a neman takarar sanata yau

An kuma bayyana cewa fitaccen malamin cocin Katolika kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Bishop Mathew Kukah, ne ya yi bitar littafin a wajen taron.

"Yadda Obasanjo ya bijire mani" - Gowon

A wani labari, mun ruwaito cewa, Yakubu Gowon ya bayyana wasu abubuwa da suka faru lokacin yakin basasa da aka yi a Najeriya a shekarun baya.

Gowon ya ce tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya taɓa ƙin yin aiki ƙarƙashin marigayi Murtala Muhammed lokacin yaƙin basasar Najeriya.

Sai dai Gowon ya ce a matsayinsa na babban kwamandan ƙasa, ya dage kan cewa yana da ikon tura jami’ai duk inda gwamnati ke buƙatarsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com