El Rufai: Kotu Ta Bada Belin Tsohon Gwamnan Kaduna, Ta Kafa Sharuda Masu Tsauri
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, beli kan kudi N100 miliyan tare da sharudda masu tsauri
- Kotu ta umarci El-Rufai ya rika zuwa hedikwatar hukumar DSS duk ranar Juma’ar karshen wata domin sanya hannu yayin da ake ci gaba da shari’a
- Kotun ta kuma ce dole ne wanda zai tsaya wa tsohon gwamnan ya kasance babban ma’aikacin gwamnati mai gida a Maitama ko Asokoro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a kan kudi har Naira miliyan 100.
Kotun ta ce dole ne Malam Nasir El-Rufai ya gabatar da mutum daya da zai tsaya masa a matsayin wanda zai karbi belinsa, mai darajar daidai da kudin belin.

Kara karanta wannan
An dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a takarar zama shugaban kasa a 2027

Source: Twitter
Sharuddan da kotu ta gindaya na belin El-Rufai
Sai dai mai shari’ar ta gindaya wasu tsauraran sharudda kafin a kammala belin tsohon gwamnan, kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna.
Kotun ta bayyana cewa dole ne mutumin da zai tsaya wa El-Rufai ya kasance mazaunin yankin Maitama ko Asokoro a Abuja.
Haka kuma dole ne ya ajiye asalin takardar mallakar gida ko fili a ofishin kotu, sharadin da kotu ta saba amfani da shi a manyan bukatun bada beli.
Mai shari’ar ta kara da cewa dole ne wanda zai tsaya wa El-Rufai ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya wanda bai gaza mataki na 17 ba.
An kuma bukaci ya gabatar da shaidar biyan albashi na akalla watanni uku tare da wasikar tabbatarwa daga manajan banki a yankin da kotun ke da iko.
Kotu bukaci karin takardu
A bangaren takardun da kotu take nema, an umurci wanda zai tsaya wa El-Rufai da ya gabatar da takardar shaidar amincinsa daga maaikata, hukuma ko sashen da yake aiki tare da shaidar biyan haraji na watanni shida da suka gabata.
Bugu da kari, an bukaci shi kansa Malam Nasir El-Rufai da ya gabatar da wasikar shaidar amincinsa daga shugaban majalisar sarakunan jihar Kaduna.

Source: Twitter
El-Rufai zai rika zuwa DSS
A matsayin daya daga cikin sharuddan belin, kotun ta umarci El-Rufai da ya mika duk wasu fasfo dinsa na kasa da kasa a ofishin kotu.
Hakazalika, kotun ta umurce shi da ya rika zuwa hedikwatar hukumar DSS duk ranar Juma’ar karshen wata da karfe 10:00 na safe domin sanya hannu a rajista har sai an kammala shari’ar.
Mai shari’a Abdulmalik ta gargadi tsohon gwamnan na Kaduna cewa idan har ya gaza cika daya daga cikin wadannan sharuddan, to za ta soke belin kai tsaye.
Asali: Legit.ng
