1975: Yakubu Gowon Ya Fadi Sunayen Wadanda Suke da Hannu a Yi Masa Juyin Mulki

1975: Yakubu Gowon Ya Fadi Sunayen Wadanda Suke da Hannu a Yi Masa Juyin Mulki

  • Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana yadda wasu jami’an da ya amince da su suka kifar da gwamnatinsa a 1975
  • Gowon ya ce tsohon kwamandan tsaron fadarsa, Joseph Garba, da wasu jami’ai na cikin wadanda aka sanar masa sun shirya juyin mulkin
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana yadda ya samu labarin hambarar da gwamnatinsa yayin taron OAU a Uganda daga bakin Shugaba Idi Amin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya bayyana yadda wasu jami’an soja da ya yarda da su suka juya masa baya tare da hambarar da gwamnatinsa a 1975.

Gowon, wanda ya mulki Najeriya tsakanin shekarar 1966 zuwa 1975, ya ce ya yi imanin cewa jami’an da ke kusa da shi suna tare da manufofinsa saboda irin kusancin da suke da shi.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya magantu kan 'barazanar' Jonathan ga takararsa da Kwankwaso

Yakubu Gowon ya tuno yadda makusantansa suka yi masa juyin mulki a 1975
Janar Yakubu Gowon a dakin taron kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa a Abuja. Hoto: @officialSKSM
Source: Twitter

Yadda aka hambarar da Yakubu Gowon a 1975

Sai dai daga baya ya gano cewa wasu daga cikinsu suna cikin wadanda suka shirya juyin mulkin da ya kifar da gwamnatinsa, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Rahoto ya nuna an hambarar da gwamnatin Gowon ne a ranar 29 ga watan Yulin shekarar 1975 yayin da yake halartar taron kungiyar OAU karo na 12 a Kampala, kasar Uganda.

Gowon ya ce yana zaune a wurin taron ne shugaban Uganda na lokacin, Idi Amin, ya karaso ya nuna masa rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kifar da gwamnatinsa.

Lamarin ya kawo karshen mulkinsa tare da ritayarsa daga aikin soja bayan sabuwar gwamnatin mulkin soja ta karbi iko.

Gowon ya samu bayanan sirri

A cikin littafinsa mai suna My Life of Duty and Allegiance, Gowon ya bayyana cewa shugaban tsaronsa kuma shugaban sashen binciken sirri na rundunar S.B, M.D. Yusuf, ya gargade shi cewa wasu jami’an soja na shirya masa juyin mulki.

Kara karanta wannan

Mutane sun barke da dariya da Jonathan ya kira Sarkin Kano Sanusi II da wani suna a taro

A cewarsa, Yusuf ya bayyana sunayen Joseph Garba, kwamandan rundunar tsaron fadar shugaban kasa, da Anthony Ochefu, shugaban rundunar ‘yan sandan NMP, a matsayin manyan masu hannu a shirin.

Janar Yakubu Gowon ya ce wannan bayani ya girgiza shi saboda mutanen biyu na daga cikin jami’an da ya fi yarda da su.

“Ba wai na san su sosai ba ne, har ma na amince da su a tsawon shekaru. Dukkansu Kiristoci ne kuma daga tsohuwar jihata ta Benue Plateau,” in ji Gowon.

Ochefu ya guje wa haduwa da Gowon

Gowon ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirrin, ya kira jami’an biyu domin jin ta bakinsu. Ya ce Joseph Garba ya amsa kiransa, amma Anthony Ochefu ya ki zuwa duk da yawan sakonnin da aka aika masa.

Ya ce kin bayyana da Ochefu ya yi ya kara tabbatar masa da cewa akwai yiwuwar shirin juyin mulkin gaskiya ne.

Duk da gargadin da ya samu, Gowon ya ce bai fasa tafiya Uganda ba saboda ya riga ya dauki alkawarin halartar taron OAU.

Sai dai ya ce bayan isa Uganda ya kasa samun nutsuwa, lamarin da ya sa ya umurci ADC dinsa ya koma Legas domin sa ido kan abubuwan da ke faruwa, cewar wani rahoto da Vanguard ta taba ruwaito wa.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga zargin yana yi wa Tinubu aiki a NDC

An kaddamar da littafin tarihin rayuwar Janar Yakubu Gowon a Abuja.
Tsofaffin shugabannin Najeriya da Sarkin Musulmi, da Kashim Shettima a taron kaddamar da littafin rayuwar Yakubu Gowon. Hoto: @stanleynkwocha_/X
Source: Twitter

Yadda Gowon ya samu labarin juyin mulkin

Gowon ya ce a rana ta uku ta taron ne ya samu tabbacin cewa an kifar da gwamnatinsa.

Juyin mulkin ya bai wa Janar Murtala Muhammed damar zama shugaban kasa, yayin da Olusegun Obasanjo ya zama shugaban ma’aikatar hedikwatar koli.

Tsohon shugaban kasar ya ce ko bayan samun labarin juyin mulkin, da farko bai yarda cewa Joseph Garba na cikin masu shirya shi ba.

Ya bayyana cewa rahoton farko na Reuters ya ambaci sunan “Colonel Darwa”, wanda ya yi zargin wata kuskuren furuci ne na sunan Garba.

“Na yi tunanin watakila masu shirya juyin mulkin sun matsa wa Garba ne ko suka razana shi cewa idan bai shiga cikinsu ba za su kashe shi.”

- Yakubu Gowon.

Danjuma, Dangote sun sayi littafin Gowon

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Danjuma ya bayar da gudunmawar N3bn a wajen kaddamar da littafin tarihin Yakubu Gowon.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Malamin addini da matarsa sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Shi ma attajirin Afrika, Aliko Dangote, ya bayar da Naira miliyan 500 domin sayen kwafi 25 na littafin tarihin tsohon shugaban kasar.

Kashim Shettima da manyan jami’an gwamnati da na soja sun halarci taron kaddamar da littafin da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com