Rana ba Ta Karya: Umarnin da Tinubu Ya ba INEC da 'Yan Sanda kan Zaben Osun

Rana ba Ta Karya: Umarnin da Tinubu Ya ba INEC da 'Yan Sanda kan Zaben Osun

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci INEC ta yi amfani da zaben gwamnan Osun wajen nuna shirinta na babban zaben 2027
  • Mai girma Bola Tinubu ya kuma umarci jami’an tsaro su tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana da gaskiya
  • ’Yan takara 15 ne za su fafata a zaben gwamnan Osun da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi amfani da zaben gwamnan jihar Osun wajen nuna irin shirinta na babban zaben 2027.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci jami’an tsaro da ke da hannu a zaben da su tabbatar da an gudanar da shi cikin lumana, gaskiya da tsari.

Sakon Tinubu ga INEC kan zaben Osun
Mai Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya a shafinsa na X ranar Juma'a, 14 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Davido ya kira ruwa, gwamnati ta yi masa tatas kan mika korafi gaban Trump

Za a yi zaben gwamna a Osun

Al’ummar jihar Osun za su fito rumfunan zabe ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026, domin zaben sabon gwamna a zaben da ’yan takara 15 ke fafatawa.

Daga cikin ’yan takarar akwai gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke na Accord Party, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, da dan takarar African Democratic Congress (ADC), Hon. Najeem Salaam, da sauran ’yan takara.

Tinubu ya bukaci INEC ta yi adalci

A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya kuma bukaci al’ummar Osun su fito su sauke nauyin da ke kansu.

Ya bukaci masu kada kuri’a da su “guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da zaben cikin lumana”, tare da tabbatar musu da cewa za a kare lafiyarsu kafin da bayan zaben.

"Yayin da al’ummar jihar Osun ke zuwa rumfunan zabe domin zabar wanda zai shugabance su na tsawon shekaru hudu masu zuwa, ina kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa da ta tabbatar da an gudanar da zaben cikin tsari."

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: 'Hanyar da APC za ta bi don lashe zaben gwamnan Osun'

“Dole ne zaben ya kasance cikin gaskiya, ’yanci da adalci. Ina kira ga INEC da ta tabbatar da sahihancin tsarin.”
Tinubu ya kara cusa wa INEC nauyin yin amfani da zaben gwamnan Osun wajen nuna irin shirinta na babban zaben 2027.
“Dole ne INEC ta yi amfani da wannan zabe na karshe da ba a gudanar tare da sauran zabubbuka ba a matsayin gwaji, domin nuna wa ’yan Najeriya cewa ta shirya tsaf domin zaben 2027,”

- Bola Tinubu

Tinubu ya umarci jami’an tsaro

Shugaban ya ce ya umarci Sufeto-Janar na ’yan sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro da za su shiga aikin zaben da su samar da cikakken tsaro a rumfunan zabe.

“Na umarci Sufeto-Janar na ’yan sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro da ke shiga zaben da su samar da cikakken tsaro a rumfunan zabe. Bai kamata a bai wa masu neman tada hankali damar kawo cikas ga tsarin ba."
“Dole ne a kare jami’an zabe da masu kada kuri’a domin su gudanar da nauyin da ke kansu na kasa ba tare da tsoro ko razana ba."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya yi gargadi mai zafi ga INEC, Tinubu kan zaben Osun

“Ya kamata masu kada kuri’a su samu kwarin gwiwar fita da yawa domin su zabi dan takarar da suke so, kasancewar an dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da zabe cikin lumana, ’yanci da adalci."
“Dole ne zabukanmu su kasance sahihai, kuma sakamakon zaben gwamnan Osun ya kasance abin da ya nuna muradin al’ummar jihar,” in ji Shugaba Tinubu."

- Bola Tinubu

Tinubu ya yi maganar zaben Osun
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Atiku ya gargadi Tinubu, INEC kan Osun

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), hukumomin tsaro da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan zaben gwamnan Osun.

Atiku Abubakar ya gargade su kan mayar da zaben gwamnan Osun tamkar aikin soja ko amfani da hukumomin gwamnati domin amfanin jam’iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng